Binciken CGTN Kan Alakar Sin Da Jamus: Ana Hada Karfi Da Karfe Daga Nesa Da Samun Aminci Cikin Lokaci
[ad_1]
Shugaban gwamnatin Jamus Merz ya fara ziyarar aiki ta farko a kasar Sin tun bayan fara wa’adin mulkinsa. Bayan ziyarar da shugabannin Faransa, Ireland, Finland, da Burtaniya suka kawo kasar, shi ne shugaba daga Turai na baya-bayan nan da ya ziyarci Sin cikin watanni uku da suka gabata.
Yadda Sin da Turai za su yi aiki tare don magance rashin tabbas a fagen kasa da kasa yana jan hankula sosai. Wani bincike da CGTN ta gudanar a duniya ya nuna cewa kashi 83.9 cikin dari na wadanda suka bayyana ra’ayoyinsu sun yi imanin cewa kasashen Turai da ke neman hadin gwiwa da Sin na taimakawa wajen magance rashin tabbas a yanayin da kasa da kasa ke ciki.
Yanayin kasa da kasa na yanzu yana fuskantar manyan sauye-sauye. A matsayinsu na manyan kasashe masu tasiri, ya kamata Sin da Jamus su yi aiki tare a yayin da ake fuskantar sauyi da kuma rudani, da shawo kan matsaloli tare, sannan su karfafa gyaran tsarin jagorancin duniya.
A cikin binciken, kashi 79.8 cikin dari na wadanda suka amsa tambayoyi sun yi imanin cewa, ya kamata Sin da Jamus su yi aiki tare don kare tsarin mabambantan bangarori da kuma cinikayya cikin ’yanci, tare da hada karfi da karfe wajen neman tabbatar da amfani da tsarin mabambantan bangarori na hakika. Bugu da kari, kashi 77 cikin dari sun ce dangantaka mai ma’ana kuma ta gaskiya da gaskiya tsakanin Sin da Jamus na kara yawaita tsammanin samun kwanciyar hankali a yanayin kasa da kasa mai fama da tashin-tashina.
An wallafa binciken ne a dandalolin CGTN na Turanci, Sifaniyanci, Faransanci, Larabci, da Rashanci, kuma cikin sa’o’i 24, jimillar mutane 12,990 sun kada kuri’a tare da bayyana ra’ayoyinsu. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
[ad_2]
Source link