Harajin Trump: Kaikayi Ya Koma Kan Mashekiya
[ad_1]
Haramta kare-karen harajin kwastam da kotun kolin Amurka ta yi ga gwamnatin shugaba Trump kwanan nan, ta haifar da zafafan sharhohi daga masana shari’a da tattalin arziki, da masu lura da manufofin kasashen waje wadanda ke ganin hukuncin ya zarce batun gyara kuren nuna karfin iko a baibai.
Lamarin yana nuna damuwa mai zurfi, ba kawai game da tsarin gudanarwa bisa doka ba har ma da sha’anin huldar kasar a fagen kasa da kasa musamman kan abin da ya shafi cinikayya.
Hausawa kan ce, “idan mutum ya ce zai ba ka riga ka duba ta wuyarsa”, akwai kasashe da dama wadanda Amurka ke musu katsalandan a harkokinsu na cikin gida game da wai ba su bin doka, inda take amfani da gaban-kai da babakere wajen tayar musu da zaune tsaye, sai dai watakila an rufe bakin tsanya yanzu tun da ga misali nan a kanta.
Abokan hulda na duniya suna sa ido sosai kan yadda Amurka ke fassara da kuma aiwatar da nata dokokin, musamman a cikin harkokin kasuwanci. Shi ya sa soke wata babbar manufa kamar ta tsarin biyan haraji bisa hujjar kakabata ta haramtacciyar hanya, yana haifar da tambayoyi a kasashen waje game da dogaro da alkawurran da Amurka ta dauka a kawancenta.
Gwamnatocin kasashen waje da kasuwannin duniya suna la’akari da tsayayyun manufofin Amurka ne da aka kafa bisa doka, ke nan matakai da ayyukan da Amurka ke aiwatarwa da suka saba wa dokokin cikin gida, za su iya raunana amincinta a tattaunawar kasa da kasa. Idan ana daukar shugaban kasar a matsayin wanda yake karan-tsaye ko watsi da iyakokin doka na gida, hakan zai yi matukar tasiri a cikin mu’amala da abokan hulda, da abokan ciniki, da kuma cibiyoyin da suka hade mabambantan bangarori.
Babu makawa, hukuncin kotun kolin zai sake fasalin harkokin kasuwanci a duniya, duk da wata dokar zartaswa ta karin haraji da kaso 15 cikin dari da shugaba Trump ya sake rattaba hannu a kai, jim kadan da ayyana hukuncin. Kasashen da harajin ya shafa na iya sake tantance dabarunsu a yanzu, yayin da wasu kuma ke kallon hukuncin kotu a matsayin wata alama dake nuna cewa cibiyoyin hukuma a Amurka na da karfin dakile yin gaban-kai wanda ta wata fuskar kuma, hakan na da muhimmanci ga ba da tabbaci ga tsarin tattalin arzikin duniya.
Gwamnatin Trump ta kakaba kare-karen haraji marasa kan gado wanda wani shugaba bai taba yi ba a kasar da nufin wai cike gibin ciniki, amma maimakon hakan, sai gibin ya zama wagege, daga bisani kuma aka soke haramtattun kare-karen harajin, abin da gwamnatin ta shuka wa kasashe ya koma mata, lamarin da ke nuna kaikayi ya koma kan mashekiya! (Abdulrazaq Yahuza Jere)
[ad_2]
Source link