Jami’an tsaro sun kama Sowore saboda shirya zanga-zanga

[ad_1]



Jami’an ‘yan sandan Najeriya sun kama ɗan gwagwarmayar nan, Omoyele Sowore, bisa ci gaba da zanga-zangar neman a saki shugaban haramtacciyar ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu.

Sowore, wanda aka kama a ranar Alhamis a birnin Abuja, wasu jami’ai dauke da bindiga ne suka yi masa dirar mikiya, sannan suka tafi da shi zuwa wani wuri da ba a bayyana ba tukuna.

Lauya mai kare haƙƙin ɗan adam kuma mai rajin kare ’yancin jama’a, Deji Adeyanju, ya tabbatar da faruwar lamarin ga wakilinmu.

“Eh, Sowore yanzu haka ’yan sanda sun kama shi,” in ji shi.

Har yanzu ba a bayyana dalilin da ya sa aka kama shi ba, amma an ji wasu daga cikin jami’an na cewa an tafi da shi ne saboda ci gaba da tayar da hankalin jama’a.

A ranar Alhamis ce dai Sowore ya jagoranci shirya zanga-zangar neman a saki mai fafutukar neman kafa ƙasar Biafra, Nnamdi Kanu, inda daga bisani jami’an tsaro suka tarwatsa su.

Bayan kammala zanga-zangar dai, jami’an tsaron sun kuma kama kanin Kanu da kuma lauyansa.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *