Harin ’yan bindiga ya yi ajalin mutum 15 a Katsina

[ad_1]



’Yan bindiga da ake zargin masu satar dabbobi ne sun kashe mutane 15 tare da jikkata wasu da dama a hare-haren da suka kai a ƙauyukan Kadobe da Falale da ke Ƙaramar Hukumar Jibiya a Jihar Katsina.

Rahotanni sun ce maharan, waɗanda ba a tantance adadinsu ba, sun kai harin ne da rana tsaka a wannan Talatar, inda suka riƙa harbi kan mai uwa da wabi.

An ce harin na iya kasancewa na ramuwar gayya, bayan zargin cewa wasu ’yan sa-kai a yankin sun kai wa maharan hari a baya.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Nasiru Ma’azu Danmusa, ya bayyana cewa jami’an tsaro sun garzaya wurin domin ɗaukar matakin gaggawa, sai dai bai tabbatar da kama kowa daga cikin maharan ba a lokacin.

Sai dai kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Abubakar Sadiq Aliyu, ya ce an samu nasarar cafke mutane uku da ake zargin suna da hannu a harin, waɗanda aka ce sun fito daga birnin Gusau na Jihar Zamfara.

Ƙaramar Hukumar Jibiya na daga cikin yankunan da aka taɓa ƙulla yarjejeniyar sulhu da ’yan bindiga a baya ƙarƙashin jagorancin Audu Lankai, lamarin da aka samu zaman lafiya na ɗan lokaci.

Wani mazaunin yankin, Alhaji Salisu, ya ce tun bayan sulhun ba a sake samun irin wannan mummunan hari ba, lamarin da ya sa jama’a ke tambayar ko sulhun na neman rushewa ko kuma wasu sabbin ƙungiyoyi ne ke ƙoƙarin tada zaune tsaye.

Harin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da fuskantar ƙalubalen tsaro a yankunan Arewa maso Yammacin Najeriya.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *