Tinubu Ya Buƙaci Gwamnoni Su Tallafa Wa Talakawa Tare Da Inganta Haɗin Kai
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci gwamnoni da shugabannin addini su ƙara tausaya wa talakawa da marasa galihu a faɗin ƙasar nan.
Ya yi wannan jawabi ne a Abuja yayin wani taron buɗa-baki a tsakanin mabiya addinai da gwamnoni.
- Sojoji Sun Daƙile Hare-haren Boko Haram, Sun Kashe Mutane 29 A Borno, Yobe
- Zaben 2027: Jam’iyyun Siyasa Sun Bayyana Shirinsu Yayin Da INEC Ta Fitar Da Jawalin Zabe
Tinubu ya ce lokutan azumin Ramadan na tunatar da muhimmancin haɗin kai, sadaukarwa da jin-ƙai.
Shugaban ya buƙaci shugabanni su tsara manufofi da za su inganta rayuwar jama’a, rage talauci, tare da bai wa matasa ƙarin damammaki.
Ya kuma ce gwamnati na shirin kafa ‘yansandan jihohi domin taimakawa wajen yaƙi da rashin tsaro.
Tinubu ya yaba wa wasu gwamnoni kan ƙoƙarinsu, yana mai cewa ƙasar na samun ci gaba.
Ya ƙara da cewa idan shugabanni suka ci gaba da aiki tare tare da mayar da hankali kan tallafa wa jama’a a matakin ƙasa, makomar Nijeriya za ta yi kyau.
Ya kuma ƙarfafi shugabanni su kasance masu haƙuri da rungumar kowa, yana jaddada cewa ci gaba ya kamata ya amfanar da kowa ba tare da la’akari da addini, ƙabila ko matsayi ba.