An buƙaci tsige shugaban APC na Kuros Riba
[ad_1]
Shugabannin jam’iyyar APC a matakin unguwanni 35 da sakatarorinsu a faɗin Jihar Kuros Riba, sun nemi a tsige shugaban jam’iyyar na jihar, Mista Alphonsus Eba, bisa zargin badaƙala da kuɗaɗen jam’iyya da kuma nuna son kai wajen gudanar da harkokin jam’iyyar.
Wannan buƙatar ta fito ne a cikin wata sanarwa da shugabanni da sakatarorin jam’iyyar suka rattaba wa hannu bayan taron da suka gudanar a garin Kalaba, babban birnin jihar, a ranar Talata.
Shugabannin sun bayyana cewa idan ba a ɗauki mataki kan shugaban ba, akwai yiwuwar rikicin cikin gida ya durƙushe jam’iyyar a jihar.
Da yake jawabi bayan taron, shugaban ƙungiyar shugabannin, Cif Kelvin Njong, ya shaida wa Aminiya cewa sun gamsu cewa shugaban jam’iyyar na jihar yana amfani da dukiyar jam’iyya yadda yake so ba tare da tuntubar kowa ba.
“Muna zargin shugaban jam’iyyar da wadaƙa da kuɗaɗen jam’iyya. Ba ya bin tsarin jam’iyya kuma ba ya jin shawarar kowa. Wannan ne dalilin da ya sa muke son a sauke shi domin a samu shugabanci nagari,” in ji shi.
Sun kuma zargi shugaban jam’iyyar da nuna bambanci da son kai ga wasu ’ya’yan jam’iyyar, lamarin da suka ce ya saɓa wa wasu sassa na kundin tsarin mulkin jam’iyyar APC da aka sabunta a watan Maris na 2022.
Haka kuma, shugabannin sun yi zargin cewa Alphonsus Eba ya ƙi raba kuɗaɗen da aka samu daga sayar da fom ga ‘yan takara a zaɓen 2023 yadda ya kamata, musamman ga shugabannin jam’iyyar a ƙananan hukumomi da mazabu.
“Akwai shugabanni da sakatarori har mutum 5,778 a matakai daban-daban, amma an ce naira miliyan 9.2 kawai aka raba daga cikin miliyoyin da aka tara.
“Shugabannin jiha su kaɗai ne aka bai wa naira miliyan 40. Wannan rashin adalci ne kuma ya saba da tsarin jam’iyya,” in ji su.
Sun kuma buƙaci a gudanar da cikakken bincike kan yadda shugaban ya riƙa kashe kuɗaɗen jam’iyya da sunan ayyuka, tare da buƙatar a tabbatar da raba kaso 70 cikin 100 na kuɗaɗen jam’iyya ga ƙananan hukumomi, mazabu, da gundumomi.
Ɗaya daga cikin shugabannin jam’iyyar a ƙaramar hukumar Bekwarra, Kwamared Odama Thomas Odama, ya ce: “Abin da muke cewa gaskiya ne, ba bita-da-ƙulli muke yi masa ba. Shugaban ya ci amana kuma hakan ya jawo ɓacin ran ’ya’yan jam’iyyar.”
Shi ma sakataren ƙungiyar shugabannin jam’iyyar APC a matakin ƙananan hukumomi, William Book, ya jaddada cewa duk zarge-zargen da aka ambata gaskiya ne.
“Ba zargin na shaci faɗi muke yi masa ba, akwai hujjoji da takardu da ke tabbatar da abin da muke faɗi,” in ji shi.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link