An Bude Cibiyar Yada Labarai Ta Tarukan NPC da CPPCC Ta Bana A Yau Juma’a

[ad_1]

Za a bude taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama’ar Sin(NPC) a karo na 14 da kuma na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta Sin (CPPCC) a karo na 14 a ranar 5 ga watan Maris da kuma ranar 4 ga watan Maris bi da bi, a birnin Beijing. A yau Juma’a, wato ranar 27 ga watan Fabrairu, cibiyar yada labarai ta wadannan manyan tarukan 2 dake Beijing ta fara aiki a hukumance, don ba da hidima ga ‘yan jarida na cikin gida da na kasashen waje da za su halarci tarukan.

Ya zuwa yanzu dai, ‘yan jarida fiye da 3000 sun yi rajistar neman ba da rahoto kan tarukan biyu, wadanda suka hada da ‘yan jarida na cikin gida fiye da 2000, da kuma ‘yan jarida na yankin Hong Kong da Macau da Taiwan da na kasashen waje fiye da 1000.(Amina Xu)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *