“Abokai Iri Uku” Za Su Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Jamus
[ad_1]
Jiya Alhamis, a yayin da shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz yake ziyara a fadar sarakuna ta kasar Sin wato the Forbidden City, ya rubuta fatansa cewa, “Ina fatan bana za ta zama shekarar hadin gwiwa da bunkasuwar kasashen Sin da Jamus”. A matsayin daya daga cikin manyan shugabannin nahiyar Turai da suka yi ziyarar aiki a kasar Sin, Friedrich Merz ya kwashe kwanaki biyu yana ziyara a birnin Beijing da birnin Hangzhou na kasar Sin, inda ya cimma sakamako masu gamsarwa da dama. Haka kuma, wakilai na kamfanonin kasar Jamus wadanda suka yi ziyara tare da mista Merz sun bayyana cewa, kasuwannin kasar Sin su ne muhimman hanyoyi a gare su domin cimma moriya da raya harkokin yin kirkire-kirkire, shi ya sa, suke son kara zuba jari a kasar Sin, don samun damammakin neman ci gaba, ganin yadda kasar Sin take neman zamanantar da kanta.
Cikin shekaru da dama da suka gataba, wani irin tsokacin dake cewa, ya kamata a kawar da barazanar da kasar Sin ta haifar ya bata fahimtar siyasa a tsakanin kasar Sin da kasar Jamus. Kafin wannan ziyarar aiki, mista Merz ya bayyana wa kafofin watsa labarai na kasar Jamus cewa, kasar Sin ta riga ta kasance muhimmiyar kasa a duk fadin duniya, kuma ba za a iya warware wasu matsalolin duniya ba, in babu taimakon kasar Sin. Kana, ra’ayin katse hulda a tsakanin kasarsa da kasar Sin kuskure ne. Yana mai cewa, zai yi illa ga ita kanta kasarsa. Wannan ya nuna cewa, kasar Jamus ta daidaita manufarta game da kasar Sin kamar yadda ake fatan gani.
A ganin kasar Jamus, yadda kungiyar tarayyar kasashen Turai wato EU ta raya huldar cinikayya mai inganci da kasar Sin, ya biya bukatun bangarorin biyu, tare da samar da zaman lumana da ci gaban duniya. Lamarin da ya ba da amsa game da tambayar da ake yi cewa, me ya sa, tun daga karshen shekarar 2025, shugabannin kasashen Turai da suka hada da na kasashen Faransa, da Ireland, da Finland, da Burtaniya, da kuma Jamus da dai sauransu, suka yi ziyarar aiki a kasar Sin daya bayan daya. (Mai Fassara: Maryam Yang)
[ad_2]
Source link