Ma’aikatar Muhallin Halittu Ta Sin: Ingancin Iska a Duk Fadin Kasar A 2025 Ya Kasance Mafi Kyau

[ad_1]

Ma’aikatar muhallin halittu ta kasar Sin ta kira taron manema labarai da safiyar yau Juma’a, inda ta gabatar da cikakken bayani game da yadda kasar ta yi kokarin kyautata ingancin iska. A cewar bayanin, a shekara ta 2025 ingancin iska a duk fadin kasar ya kai matsayi mafi kyau tun farkon fara sa ido.

A cikin ma’auni 3 na tantance ingancin iska na shekara ta 2025, matsakaicin yawan ma’aunin gurbatar iska na PM2.5 ya kai maki 28 μg/m³, adadin kwanakin da iska ta kasance mai kyau ya kai kashi 89.3 cikin 100, kuma adadin kwanakin da gurbacewar iska ta yi tsanani ya kai kashi 0.9 cikin 100, adadin da duk suka kai matsayi mafi kyau tun farkon fara sa idon.

A lokacin aiwatar da shirin raya tattalin arziki da zamantakewar al’ummar Sin na shekaru biyar-biyar karo na 14, wato daga shekarar 2021 zuwa ta 2025, kasar Sin ta ba da fifiko kan yaki da gurbatar iska bisa aiki da kimiyya da kuma doka, tare da karfafa karfin kiyaye ingancin iska. Kuma ta kara kyautata iska a manyan bangarori 3 wato masana’antu da makamashi da sufuri, inda suka karkata zuwa hanya mai tsabta da rage fitar da hayaki mai dumama yanayi, da gina tsari mafi girma a duniya ta fuskar samar da wutar lantarki mai tsabta da na samar da karfe. Kazalika, yawan motoci masu amfani da wutar lantarki da aka samarwa da kuma sayarwa ya ci gaba da zama na farko a duniya a cikin tsawon shekaru 11 a jere.

Bugu da kari, a lokacin shirin karo na 14, matsakaicin yawan PM2.5 a duk fadin kasar ya ragu da kashi 20 cikin 100, kuma yawan GDPn kasar Sin ya karu da kashi 30 cikin 100, wanda ya nuna cewa Sin ta samu nasarar kare muhallin halittu da ci gaban tattalin arziki tare.(Amina Xu)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *