Mahaddata 7 sun samu kyautar motoci a gasar Alƙur’ani a Abuja

[ad_1]



Mahaddata bakwai sun samu kyautar motoci a gasar karatun Alƙur’ani ta ƙasa da ƙungiyar Izala ta shirya, wadda aka kammala a ranar Lahadi a Abuja.

Wakilai daga jihohi 25 na Najeriya ne, suka halarci gasar, inda suka fafata a fannoni daban-daban na haddar Alƙur’ani da tafsiri.

An gudanar da gasar ne a Babban Masallacin Ƙasa da ke Abuja.

Babban sakataren gasar Alƙur’ani ta Izala, Alhafiz Abdulmumini Aliyu, ya bayyana cewa Aliyu Abdurrahman daga Jihar Kaduna ne ya zama zakaran gasar baki ɗaya.

Ya yi fice ne a ɓangaren haddar Alƙur’ani izu 60 tare da tafsiri.

An ba shi kyautar babbar mota, tare da kuɗi, tufafi da littattafan Addinin Musulunci.

Sauran mutane shida da suka samu motoci sun haɗa da Abdullahi Salisu Yahaya da Idris Saminu Ash’hab daga Jihar Kano, da kuma Mahmood Muhammad daga Jihar Sakkwato, waɗanda suka yi nasara a fannoni daban-daban.

Haka kuma, an karrama waɗanda suka zo na biyu, na uku, na huɗu da na biyar a fannoni kamar izu huɗu, izu 10, izu 40 da izu 60, inda aka ba su kyaututtuka kamar babura da sauransu.

Shugaban Majalisar Malamai na Ƙasa na Izala, Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir, ya gode wa waɗanda suka tallafa wa gasar.

Ya gode wa Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, wanda ya bayar da motoci biyu, da Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, wanda ya bayar da tallafin Naira miliyan 40.

Sauran da suka tallafa wa gasar sun haɗa da ’yan Majalisar Wakilai daga Jihohin Kano da Borno, wato Abubakar Kabir Bichi da Muktar Aliyu Betara, waɗanda kowanensu ya bayar da Naira miliyan 50.

Shugaban kwamitin kuɗi da ayyuka na gasar, Honorabul Ahmad Idris Wase, ya ce wasu manyan shugabanni sun yi alƙawarin bayar da gudummawa, ciki har da Kakakin Majalisar Wakilai, Abbas Tajuddeen.

Sauran sun haɗa da Gwamnan Jihar Gombe, Inuwa Yahaya, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, da Sanata Abubakar Yari.

Shi ma Ahmad Idris Wase, ya bayar da Naira miliyan 10, yayin da Mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ya bayar da Naira miliyan 10.

A saƙon da Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya aike ta hannun Sarkin Bwari, Alhaji Muhammad Auwal Ijakoro, ya taya waɗanda suka yi nasara murna.

Ga hotunan yadda gasar ya kammala:


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *