EFCC ta tsare Mele Kyari kan binciken matatun mai




Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arziƙi Zagon Ƙasa (EFCC), ta tsare tsohon Shugaban Hukumar Man Fetur ta Ƙasa (NNPC), Mele Kyari kan zargin karkatar da kuɗaɗen gyaran matatun man Najeriya.

Kyari na cikin jerin waɗanda ta hukumar ta sanya ido a kansu, kuma ta isa ofishin EFCC da misalin ƙarfe 2:30 na ranar Laraba.

Majiyoyi, sun bayyana cewar ya isa ne don bayar da bayanai kan batutuwan kuɗi da aka ware don gyaran matatun man fetur a Najeriya lokacin da yake shugabantar NNPC.

Wani majiya ta shaida wa Aminiya cewa: “Eh, yana ofishinmu. Za a kai shi ɗaki inda masu bincike na EFCC za su yi masa tambayoyi.”

A baya, wata kotun tarayya a Abuja ta bayar da umarnin kulle dukkanin asusun bankin Kyari, domin bai wa EFCC damar gudanar da bincike a kansa.

Ana sa ran samu ƙarin bayani daga bisani.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *