Dalilin da ya sa Tinubu ya tsaya a filin jirgin saman Jos — Fadar Shugaban Ƙasa

[ad_1]



Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana dalilan da suka sa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya gudanar da ziyararsa ta jaje a filin jirgin saman Jos maimakon shiga cikin Jihar Filato.

Fadar ta bayyana cewa matsalar na’urorin sufurin jiragen sama ne suka tilasta masa yin hakan.

Shugaban ya gana da iyalan waɗanda harin Angwan Rukuba ya shafa, inda aka kawo su filin jirgin saman domin ganawa da shi.

A yayin tattaunawar, Shugaba Tinubu ya shaida wa waɗanda abin ya shafa cewa: “Ba ku da isasshiyar wutar lantarki a nan filin jirgin, kuma dole ne na tashi nan da mintuna 10.

“Babu kuɗin da zan ba ku da zai maye abin da kuma rasa, amma na zo ne na yi muku ta’aziyya kuma na ba ku tabbacin cewa hakan ba zai sake faruwa ba.”

Sai dai ’yan adawa sun soki wannan mataki na Shugaba Tinubu, inda suke ganin ziyarar ta fi karkata wajen yin fice a kafafen sada zumunta fiye da jajanta wa waɗanda abin ya shafa.

Phrank Shaibu, mai magana da yawun tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya siffanta ziyarar a matsayin “shirin wasan kwaikwayo”.

Sai dai, Mai Taimaka wa Shugaban Ƙasa kan Harkokin Yaɗa Labarai da Tsare-tsare, Bayo Onanuga, ya kare ziyarar.

Ya ce Tinubu yana da sabogogi da yawa da ke jiransa, inda ya fara karɓar baƙuncin Shugaban ƙasar Chadi a fadar Villa kafin ya nufi Jos.

Ya ƙara da cewa tattaunawar tasu ta ɗauki tsawon lokaci fiye da yadda aka tsara, wanda hakan ya rage wa Shugaban lokacin gudanar da ayyukansa a Filato.

Onanuga ya ƙara da cewa: “Tafiya daga filin jirgi zuwa tsakiyar garin Jos tana ɗaukar kusan mintuna 40. Abin takaicin shi ne, filin jirgin Jos ba shi da na’urorin kewayawa da za su ba da damar tashi da daddare.

“Don haka, idan Shugaban Tinubu ya shiga cikin gari, ba zai samu damar tashi ya bar jihar ba kafin faɗuwar rana.”

Domin gudun kada Shugaban ya gaza komawa a kan lokaci, jami’ai sun gayyato wakilan al’umma zuwa ɗakin taro na filin jirgin saman Jos inda suka gana da shi.

A can ne Tinubu ya yi ta’aziyya tare da tattaunawa da shugabannin tsaro da na gargajiya kan hanyoyin kawo ƙarshen rikici a jihar.

Ya kuma sanar da shirin sanya na’urorin CCTV na zamani guda 5,000 don sanya idanu kan tsaro a jihar, tare da gayyatar shugabannin al’umma zuwa Abuja don tattaunawa kan samar da zaman lafiya mai ɗorewa.

Fadar Shugaban Ƙasa ta jaddada cewa ziyarar ba an yi fa nufin nuna isa ba, face wani mataki ne na ganin an tabbatar da cewa an tattauna da masu ruwa da tsaki domin samar da maslaha ta din-din-din.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *