Mutane Da Dama Sun Jikkata A Rikicin ‘Yan Daba A Kano

[ad_1]

Ana fargabar an kashe mutane da dama tare da lalata dukiyoyi, sakamakon wani rikici da ya barke a tsakanin jami’an tsaro da mazauna kauyukan Katai da Fauda a Karamar Hukumar Wudil ta Jihar Kano.

Mazauna yankin sun ce, rikicin ya samo asali ne sakamakon rikicin filaye da aka samu tsakanin wasu mutanen kauyen da wani Basaraken gargajiya na Fulani, wanda ake zargin ya yi ikirarin mallakar filaye na iyalan wasu Hausawa.

Tashin hankalin, ya ta’azzara ne bayan da rahotanni suka ce, mutanen kauyen sun ki bayar da filin.

Majiyoyin al’umma sun ce, lamarin ya kara ta’azzara ne bayan wani samame da wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton jami’an tsaro ne, suka kai cikin dare.

Shedun gani da ido sun ce, maharan sanye da kayan mufti, sun far wa kauyukan tare da bude wuta, lamarin da ya haifar da firgici a tsakanin mazauna garin da tun farko suka dauke su a matsayin ‘yan fashi.

A martanin da aka bayar an ce, mutanen kauyen sun yi artabu ta hanyar amfani da makamai na cikin gida, lamarin da ya kai ga artabu, inda aka harbe wani mazaunin garin.

Har ila yau, an ce; mutanen kauyen sun ci karfin daya daga cikin maharan, inda suka kashe shi, suna kyautata zaton dan fashi ne.

Daga baya hukumomi sun bayyana marigayin a matsayin jami’in tsaro, lamarin da ya kara dagula al’amura.

Majiyoyi sun yi zargin cewa, daga bisani jami’an tsaro sun kaddamar da farmakin ramuwar gayya, wanda ya yi sanadin asarar rayuka da kona gidaje, lamarin da ya tilasta wa mazauna yankin tserewa.

Shugaban Karamar Hukumar Wudil, Abba Muhammad Tukur, ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya bayyana lamarin a matsayin abin ban tausayi.

A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Abba Darki ya fitar, ya tabbatar wa mazauna garin cewa; ana ci gaba da gudanar da bincike, sannan kuma za a yi adalci ba tare da tsoro ko fargaba ba.

Kokarin jin ta bakin kakakin rundunar ‘yansandan Kano Abdullahi Haruna Kiyawa ya ci tura, yayin da al’ummomin da abin ya shafa ke ci gaba da kokawa.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *