An kama masu satar jarirai a Nasarawa
[ad_1]
Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Nasarawa ta samu nasarar ceto jariri dan kwana uku da aka sace tare da kama wasu mata biyu da ake zargi da hannu a cikin lamarin.
Mai magana da yawun rundunar, SP Ramhan Nansel, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar a Lafia.
Ya ce lamarin ya faru ne a safiyar Asabar, 29 ga Maris, 2026, da misalin ƙarfe 5:45 na safe, lokacin da wata mai jego, Aisha Bada mai shekara 19, mazauniyar Unguwan Bako, Orange Market, Mararaba, ta kai rahoton cewa wasu da ba a san su ba sun kutsa gidanta, suka yi mata barazana da ƙarfi, sannan suka sace jaririnta da ta haifa kwana uku kacal.
A cewar Nansel, Kwamishinan ’Yan Sanda na jihar, CP Shetima Jauro Mohammed, ya umarci jami’an bincike da su bi sahun waɗanda ake zargi.
Bayan samun sahihan bayanai, jami’an tsaro sun kama Furera Abdulrahman mai shekara 35 da Sadiya Abdullahi mai shekara 39 a safiyar 3 ga Afrilu, 2026, da misalin karfe 4:00 na safe.
Jaririn da aka sace an same shi a hannunsu, kuma an ceto shi cikin ƙoshin lafiya. Waɗanda aka kama sun amsa laifin tare da bayyana cewa suna da wani abokin aikata laifi da ya tsere.
An kai jaririn Asibitin Koyarwa na Mararaba inda aka tabbatar da lafiyarsa, sannan aka miƙa shi ga iyayensa.
Rundunar ta ce bincike yana ci gaba, tare da ƙoƙarin kamo wanda ya tsere.
Ta kuma yi kira ga jama’a da su kasance masu lura da tsaro, tare da kai rahoton duk wani abin da suka gani na zargi ga ofishin ’yan sanda mafi kusa.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link