Mamakon ruwa ya lalata gidaje 70 a Jigawa
[ad_1]
Aƙalla gidaje 70 ne suka ruguje wasu da dama suka lalace sakamakon ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da ya haddasa ambaliya a Ƙaramar Hukumar Malam Madori ta Jihar Jigawa.
Yankunan da ibtila’in ya shafa sun haɗa da Tonikutara, Gandun Sarki, Gandun Bundugoma da rukunin gidajen Shagari Quarters, bayan ruwan sama da aka kwashe sa’o’i da dama a ranar ya mamaye kwalbatoci da magudanan ruwa a yankin.
Dan-Ummah Abba, wani magidanci da lamarin ya shafa a Gandun Sarki ya bayyana cewa gidansa da yake zaune a ciki sama da shekara 30 ya rushe a sakamakon lamarin.
Daga nan ya roƙi Gwamnatin Jihar Jigawa da ta kawo musu ɗaukin gaggawa.
Ruwan saman da aka fara tun ranar Asabar har zuwa safiyar Lahadi, da ya tilasta wa mazauna yankin yin ƙaura tare da neman mafaka a wuraren ’yan uwa.
Bulama Jamilu, wani basarake a yankin, ya ce: “Yawancin waɗanda abin ya shafa suna fakewa a gidajen ’yan uwansu saboda an bar gidaje da yawa a lalace.”
Shugaban Ƙaramar Hukumar Malam Madori, Salisu Sani Garun-gabas ya jajanta wa waɗanda abin ya shafa tare da yin alƙawarin tallafin da ake buƙata ga waɗanda bala’in ya shafa .
Ya kuma sanar da kwamitin kula da agajin gaggawa na jihar da ya tantance tare da bayar da rahoton ɓarnar da aka yi a Gandun Bundugoma, Gandun Sarki, Tonikutara da Shagari Quarters.
Shugabar kwamitin agajin gaggawa na ƙaramar hukumar, Hajiya Amina Haruna Dokajo ta ce “Ɗan majalisar mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Malam Madori Hamza Adamu Babayaro ya bayar da gudunmawar motar yashi da sauran kayan agaji ga waɗanda abin ya shafa.”
Ta kuma yi bayanin cewa shugaban ƙaramar hukumar ya umlaurci kwamitin da ya kafa injin fanfo a Gandun Sarki wanda zai kwashe ruwan zuwa karkara.
Tun da farko wata tawagar gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin babban mai ba da shawara ta musamman kan ambaliyar ruwa, Hamza Muhammad Hadejia ta isa wurin da lamarin ya faru tare da yin alƙawarin ɗaukar matakin gaggawa don daƙile aukuwar hakan a nan gaba.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link