Jami’ar MDD: Kasar Sin Babbar Ginshiki Ce Ta Cinikayyar Duniya
[ad_1]
Wata babbar jami’ar cinikayya ta MDD ta bayyana cewa, yayin da rashin tabbas da karuwar kariyar cinikayya ke ci gaba da tarnake tattalin arzikin duniya, kasar Sin ta ci gaba da zama babbar ginshikin ci gaban cinikayyar duniya da tattalin arzikin duniya.
A wata hira da ta yi da kamfanin dillancin labarai na Xinhua kwanan nan, darektar sashen cinikiyyar kasa da kasa da kayayyaki na hukumar MDD mai kula da kasuwanci da bunkasa ci gaba (UNCTAD) Luz Maria de la Mora, ta yi hasashen cewa za a samu karin manyan abubuwan da za su kawo ci gaban ciniki a shekarar 2026 daga kasashe masu tasowa. Ta ce, ciniki a tsakanin kasashe masu tasowa, wadanda aka fi sani da kasuwancin kasashe masu tasowa, yanzu ya kai sama da kashi 40 cikin dari na daukacin cinikayyar duniya.
Ta yi karin haske game da manufar kasar Sin ta soke biyan haraji ga kasashen Afirka da ke da alakar diflomasiyya da kasar, inda ta bayyana hakan a matsayin wani bangare na muhimmin kokarin da ake yi na tabbatar da cewa ciniki ya ci gaba da zama ginshikin samun ci gaba.
Ta kara da cewa, a matsayin kasar Sin na babbar mai fitar da kayayyaki a duniya kuma babbar mai shigo da kayayyaki, ta zurfafa hade tsare-tsaren samar da kayayyaki da na sarrafa kayayyaki na duniya.
De la Mora ta kuma kara da cewa, ta yi imanin kasar Sin za ta ci gaba da zama babbar mai fafutukar tabbatar da ka’idojin ciniki a tsakanin bangarori daban-daban tare da taka rawa wajen taimaka wa kasashe masu tasowa a bangaren shigar da su cikin tsarin ciniki na duniya yadda ya kamata. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
[ad_2]
Source link