Tsaro: Taimakonmu Amurka ya kamata ta yi maimakon ba barazana ba — Kwankwaso
[ad_1]
Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana damuwarsa kan kalaman da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi game da Najeriya.
Kwankwaso, ya yi wannan magana ne bayan Trump ya yi barazanar ɗaukar matakin yaƙi game da zargin kisan kiyashi da ake yi wa Kiristoci.
A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Kwankwaso, ya ce Najeriya ƙasa ce mai cikakken ’yanci, wadda ke fama da matsalar tsaro daga miyagu a sassa daban-daban na ƙasar.
“Matsalar tsaron da muke fuskanta ba ta bambanta tsakanin addini, ƙabila ko ra’ayin siyasa,” in ji shi.
Ya buƙaci gwamnatin Amurka da ta tallafa wa Najeriya da sabbin fasahohi domin yaƙar matsalar tsaro maimakon yin kalaman da za su iya raba kan ’yan ƙasa.
“Amurka ya kamata ta taimaka wa hukumomin Najeriya da ingantattun fasahohi don magance matsalolin tsaro, maimakon yin barazanar da za ta ƙara raba ƙasar,” in ji Kwankwaso.
Haka kuma, ya shawarci Gwamnatin Najeriya da ta naɗa jakadu na musamman domin inganta hulɗar diflomasiyya da Amurka da kare muradun ƙasar a matakin duniya.
Ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya da su zauna lafiya, inda ya bayyana cewa wannan lokaci ne da ya dace a fifita haɗin kan ƙasa ba abin da ke raba ta ba.
“Wannan lokaci ne da ya kamata mu mayar da hankali kan abin da zai haɗa kanmu ba wanda zai raba mu ba. Allah Ya albarkaci Najeriya,” in ji shi.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link