Darussa Daga Ramadan Na 10: Zumunci Da Tausayi
[ad_1]
A cikin watan Ramalana muna koyon jin ‘yan’uwanmu a jikinmu kamar uwa ɗaya uba ɗaya. Domin a lokacin da muke azumi, muna ɗanɗanar yunwa da ƙishirwa, yanayin da yawancin mabuƙata suke rayuwa da shi a kullum. Wannan haɗin ji yana haifar da tausayi, kuma tausayi yana haifar da taimako a tsakanin al’umma.
A lokacin buɗa-baki, idan muka zauna tare da ‘yan’uwa, maƙwabta da abokai, muna jin wani irin kusanci da haɗin kai. Ko ba jininmu ɗaya ba ne, amma azumi ya haɗa zukatanmu. Yunwa ta zama ta kowa, ƙishirwa ta zama ta kowa, addu’a ta zama ta kowa. Wannan shi ne ruhin al’umma ɗaya.
- Darussa Daga Ramadan Na 9: Danne Fushi Da Nutsuwa A Ramalana
- Darussa Daga Ramadan Na 8: Haƙuri Da Sadaukarwa Domin Rabauta Ta Har Abada
Ramalana yana rusa katangar bambanci, na kuɗi, ko matsayi ko asali, ko ƙabila, ko yare, domin a gaban yunwa da ƙishirwa, dukkanmu daidai muke. Wannan daidaito yana koya mana cewa Musulumi ba ya rayuwa shi kaɗai; yana rayuwa ne a cikin al’umma. Manzon Allah (S.A.W) ya bayyana wannan ma’ana cikin hikima a hadisin da ya zo a Sahihul Bukhari cewa: “Za ka ga muminai a cikin tausayin juna, da ƙaunar juna, da tausasawa juna, kamar gangar jiki guda ɗaya; idan wata gaɓa ta yi ciwo, sai dukkan jiki ya amsa da zazzaɓi da rashin barci” Wannan misali yana da zurfin ma’ana. Idan yatsa ya ji raɗaɗi, ido ba zai ce ‘ba ruwana ba’; idan zuciya ta yi rauni, hannu ba zai ƙi taimako ba. Haka ya kamata muminai su kasance: idan wani yana cikin wahala, sauran su ji kamar wahalar tasu ce duka.
Saboda haka, taimakon mabuƙata a Ramalana ba sadaƙa kaɗai ba ce, wata hanya ce ta rayar da zuciya. Idan ka ba wa mai ji yunwa abinci, ba cikinsa ka cika kaɗai ba, zuciyarka ka tsarkake. Idan ka taimaki mai buƙata, ba matsalarsa ka sauƙaƙa kaɗai ba, zumunci ka ƙarfafa.
Yin wannan aiki yana ƙara sanya jin ‘yan’uwa a jikinmu, yana gina tausayi a zuciya, yana kuma sa al’umma ta zama mai ƙarfi. Domin al’umma mai tausayi ita ce al’umma mai ɗorewa.
Ramalana makaranta ce ta haɗin kai. Idan muka fita daga cikinsa da zuciya mai tausayi, da hannu mai bayarwa, da rai mai jin halin wasu, to mun fahimci darasinsa.
Allah Ya haɗa zukatanmu a bisa alheri, Ya sanya mu masu jin halin ‘yan’uwanmu, Ya kuma gina al’ummarmu bisa ƙauna da tausayi. Amin.
Abu Razina Nuhu Ubale Ibrahim Paki
[ad_2]
Source link