Kungiyar Jama’atu Ta Yi Tir Da Kashe-kashen Da Suka Auku A Jos

[ad_1]

Kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI), reshen Jihar Filato, ta bayyana hare-haren da aka kai wa al’ummar unguwar Rukuba da ke Karamar Hukumar Jos ta Arewa, a matsayin na dabbanci da rashin hankali, inda ta yi kira ga gwamnati da hukumomin da abin ya shafa da su gaggauta yin bincike a kan wadanda suka haddasa lamarin.

Shaidun gani da ido a ranar Lahadin da ta gabata, sun bayyana cewa; maharan wadanda suka yi amfani da babura, sun mamaye al’ummar ne da misalin karfe 7:30 na dare, a daidai lokacin da jama’a ke gudanar da harkokinsu na yau da kullum, inda suka fara harbe-harbe babu gaira babu dalili, lamarin da ya haifar da firgici a tsakanin mazauna yankin.

  • Fadar Shugaban Ƙasa Ta Soki Jami’iyyar ADC, Ta Ce Su Fuskanci Matsalolinsu
  • Mutane Da Dama Sun Jikkata A Rikicin ‘Yan Daba A Kano

Rundunar ‘yansandan Jihar Filato, ta tabbatar da kashe mutum 14 da suka hada da mata biyu, amma shugaban kungiyar matasan Berom na kasa (BYM), Barista Solomon Dalyop, ya yi ikirarin kashe mutum 27.

JNI, a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun sakatarenta, Dr. Salim Musa Umar, ta bayyana matukar kaduwarta tare da alhinin faruwar lamarin, wanda ya yi sanadiyyar asarar rayuka da dama tare da yin kakkausar suka ga harin.

Haka zalika, ta bayyana harin a matsayin na dabbanci da rashin hankali, inda ta ce; babbar barazana ce ga zaman lafiya a jihar ta Filato.

Sanarwar ta ce, “Muna matukar bakin ciki da faruwar wannan bala’i, sannan kuma bai kamata a taba keta alfarmar rayuwar Bil’adama ba a kowane hali, wannan ta’addancin ba abu ne da za a amince da shi ba, kuma wajibi ne kowa ya yi Allah-wadai da shi.”

Dakta Salim ya kuma mika ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasu tare da yin addu’ar Allah ya ji kan wadanda suka rasu, tare da yi wa wadanda suka jikkata fatan samun sauki cikin gaggawa.

Kungiyar ta kuma yi kira ga al’ummar jihar, da su kwantar da hankalinsu tare da bin doka da oda, tare da gargadin duk wani nau’in ramuwar gayya da ka iya kara ruruta wutar rikici.

JNI ta kara da cewa, “A wannan mawuyacin lokaci, muna kira ga dukkan ‘yan kasa, da su kasance masu kamun kai, kada mu bar fushi da bakin ciki su sa mu shiga aikata ayyukan da za su iya dagula mana al’amuranmu.”

Haka kuma, ta yi kira ga hukumomin tsaro da su gaggauta gudanar da cikakken bincike na gaskiya da adalci kan lamarin, da nufin zakulo wadanda suka aikata laifin da kuma gurfanar da su a gaban kuliya.

JNI ta jaddada kudirinta na inganta zaman lafiya da hadin kai da adalci a Jihar Filato da ma Nijeriya baki-daya.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *