Sheikh Al-Sudais Ya Gargadi Masu Ibadah Kan Kiyaye Darajar Masallatan Harami
[ad_1]
Daga Naziru Adam
Shugaban Harkokin Addini na Masallacin Harami da Masallacin Annabi, Sheikh Dr. Abdulrahman bin Abdulaziz Al-Sudais, ya yi tsokaci kan wani lamari da ya faru inda wani mahajjaci ya yi yunƙurin dirowa daga bene na farko a Masallacin Harami, yana mai kira ga dukkan masu ziyara da su mutunta daraja da tsarkin wuraren ibada masu alfarma.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a daren Alhamis, 25 ga Disamba, 2025, Sheikh Al-Sudais ya buƙaci masu ibada da su bi dukkan ƙa’idoji da dokokin da aka shimfiɗa, tare da kiyaye ladubban Musulunci yayin gudanar da ibada, domin samun kusanci da Allah a cikin waɗannan wurare masu tsarki.
- ‘Yansanda Sun Kama Mutane 22, Sun Ƙwato Makamai, Motoci, Da Ƙwayoyi A Faɗin Nijeriya
- Kasar Sin Ta Yi Tasiri Sosai Wajen Bunkasar Sashen Fitar Da Hajoji A Duniya
Sheikh Al-Sudais ya yi kakkausar gargadi kan duk wani yunƙuri na jefo kai daga sama a cikin masallacin, yana mai bayyana cewa hakan na daga cikin yunƙurin kashe kai, wanda Musulunci ya haramta ƙwarai inda ya ambato ayoyin Alƙur’ani da suka yi gargaɗi kan duk wani aiki da ke kai wa ga halaka kai.
Haka kuma, ya yabawa saurin ɗaukar mataki da jarumtar da jami’an tsaron Masallacin Harami suka nuna wajen shawo kan lamarin, yana mai cewa wannan ya nuna ƙwarewa da jajircewarsu wajen sauke nauyin da aka ɗora musu.
A ƙarshe, Sheikh Al-Sudais, ya jaddada cewa irin wannan ƙoƙari na nuni da ƙudirin Masarautar Saudiyya, wajen tabbatar da tsaro da mutunta tsarkin Masallatan Harami biyu, tare da yin addu’ar Allah Ya ci gaba da bayar da kariya da shiriya da kuma nasara ga dukkan masu hidima da masu ziyartar wuraren ibadar.
[ad_2]
Source link