Ƙungiyar Ƙwadago Ta Yi Barazanar Ƙauracewa Zaɓen 2027 Kan Tura Sakamako Ta Intanet

[ad_1]

Ƙungiyar Kwadago ta ƙasa (NLC) ta yi barazanar ɗaukar mataki mai tsauri, har ma ta ƙaurace wa duk wani abu da ya shafi babban zaɓen 2027, idan ba a tilasta tura sakamakon zaɓe ta intanet cikin gyaran Dokar Zaɓe ta 2022 ba.

A wata sanarwa da shugabanta, Joe Ajaero, ya fitar, ya ce dole ne a fayyace a cikin doka cewa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC) ta riƙa tura sakamakon zaɓe kai tsaye daga rumfunan zaɓe ba tare da wata rufa-rufa ba. Ya ce ’yan Nijeriya na da haƙƙin ganin tsarin zaɓe mai gaskiya da bayyane.

  • Gyaran Dokar Zabe: Yadda Jinkirin Majalisar Dattawa Zai Iya Kawo Tsaiko Ga Zaben 2027
  • Manyan Ƙalubale Takwas Da Ke Shafar Farashin Tumatir

Wannan matsaya ta biyo bayan matakin Majalisar Dattawa na ranar 4 ga Fabrairu, inda ta ƙi amincewa da shawarar tilasta wa INEC tura sakamako a ainihin lokacin da ake gudanar da zaɓe, yayin da ta bar tanadin da ke bai wa hukumar damar yin hakan ba tare da wajabta ba.

Ajaero ya ce NLC na nuna damuwa kan saɓanin bayanai da ke fitowa daga Majalisar Dattawa game da gyaran dokar, tare da buƙatar a fito fili a sanar da jama’a abin da aka amince da shi.

Ƙungiyar ta yi gargaɗin cewa rashin wajabta tura sakamako ta intanet a lokaci guda na iya haddasa rikici kafin, lokacin ko bayan zaɓe, tare da yiwuwar rage fitowar jama’a domin kaɗa ƙuri’a.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *