Buƙatar Wadata ‘Yan Nijeriya Da Wutar Lantarki A Ramadan

[ad_1]

Assalamu Alaikum Wa Rahmatullahi Ta’ala Wa Barakatuhu.

Jama’a barkanmu da shigowa wata mai girma, mai alfarma, watan Ramadana, barkanmu da kasancewa tare da wannan fili mai albarka, filin da ke zaƙulo muku batutuwan da suke ci wa al’umma tuwo a ƙwarya.

A wannan mako zan yi magana ne a kan shugabanninmu, wakilanmu, masu mulkinmu, masu sarauta, masu kuɗinmu. Idan muka yi duba a cikin shekara muna da kwana 360, a wannan kwana ɗari uku da sittin ɗin wata ɗaya ne ko na ce kwana 29 ne na watan Ramadana da musulmai suke gabatar da ibada.

  • KEDCO Ta Nuna Damuwa Kan Katsewar Wutar Lantarki A Arewa Maso Yamma
  • Samar Da Wutar Lantarki A Kaduna Wajibi Ne Ba Alfarma Ba – Gwamna

Wata ne da yake da falala da girma a wajen ubangiji, sai dai babban abin baƙin ciki da takaici, duk waɗannan mutanen da muke da su; masu mulki, masu sarauta, masu kuɗi, masu faɗa a ji a Arewacin Nijeriya, a wata ɗaya ba ma iya samu a gabatar da ibadar ubangiji. Ko da haɗuwa za su yi Arewacin Nijeriya musulmai su yi ƙoƙarin yadda za a yi a samar da wuta a watan azumin Ramadana, domin al’ummar musulmi talakawa su ji daɗin ibada, su ma su samu lada, amma ba a iya yi, wannan abun takaici ne.

Ina mai bayar da shawara waɗannan mutane shuwagabannin namu su riƙa haɗa kai, idan watan azumi ya kama za su sami lada, su ma suna so su sami rahamar ubangiji. Ita kuma wutar Nefa kamar wata rahama ce a duniya da talaka yake iya mora. Saboda sana’o’insa da komai nasa zai haɓaka a wannan wata na Ramadana, wannan ba abun lura bane ba?

Ku lura fa duk lokacin da za ku ga ana samun wuta sosai akai-akai to, Kirsimeti ce ta zo watan Disamba. To, me ya sa mu ma ba za mu yi haka ba, ku fa wakilanmu ne wakilan ƙasar mu ne. Saboda haka, wannan abun takaici ne. Kuma ina kira ga malamai su yi kira da masu hannu da shuni, shugabanni lallai su riƙa yin ƙoƙari wata na Ramadan, watan azumi ana iya samun wutar da talaka zai amfana ko da ta wata ɗaya ce.

Allah (SWT) zai yi farin ciki da wannan, amma an kau da kai, bai kamata ba a ce ana da shugabanni wakilai a Arewacin Nijeriya kuma musulmai amma ba za su iya yi wa musulunci hidimar wata ɗaya ba. Ko haɗuwa suka yi suka ce sun samar da wuta dan kawai watan azumin Ramadana, ai sun yi wa musulunci hidima za kuma su sami lada.

Muna fatan za su yi amfani da wannan dama, wannan wata da muka shiga na Ramadana su samar da wuta ga talaka da al’ummar musulmi ta Najeriya baki ɗaya su amfana.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *