An yi garkuwa da tsohon Shugaban SUBEB na Jihar Neja

[ad_1]



Tsohon Shugaban Hukumar Ilimin Bai Ɗaya ta Jihar Neja (SUBEB), Alhaji Alhassan Bawa Niworo, ya shiga hannun ’yan bindiga.

An yi garkuwa da shi tare da wasu fasinjoji da dama a yammacin Litinin, 29 ga Satumba, 2025, da misalin ƙarfe 4 na yamma, tsakanin ƙauyukan Felegi da Ibi a kan hanyar Mokwa zuwa New Bussa a Ƙaramar Hukumar Borgu.

Wata majiya ta ce Niworo tare da wasu ciki har da wani lauya, Barista Ahmad, na kan hanyarsu zuwa Minna ne lokacin da ’yan bindigar suka tare hanyar, suka kuma yi awon gaba da su cikin daji.

Wasu daga cikin waɗanda aka sace ’yan kasuwa ne da suka fito daga kasuwar mako ta New Bussa.

Manoma na tserewa

Al’ummar karkara a ƙananan hukumomin Mariga, Magama, Kontagora, Mashegu, Borgu da Rijau a yankin Neja ta Arewa maso Yamma na ci gaba da barin gidajensu saboda hare-haren da suka ƙaru a kwanaki biyar da suka wuce.

Da sanyin safiyar Talata, ’yan bindiga fiye da 200 sun kutsa garin Ibeto a da aka Magama, abin da ya tilasta mazauna su tsere.

A wani bidiyo da wani mazaunin ya yada, an nuna mata da yara suke gudun hijira cikin duhu da fitilun hannu.

Wata majiya ta ce: “Da tsakr dare suka kai hari a Dogon-Daji, Ugulu, Maira, Atabo da Ibeto. Sun kuma shiga Lioji kafin su dawo su kai farmaki a Maira, Ugulu, Atabo da Ibeto. A Atabo, sun yi awon gaba da mutane da dama bayan sun kasa samun shanu da za su sace.”

Majiyar ta ƙara da cewa, “Mazauna Ibeto sun tsere kafin daga bisani ’yan bindigar su mamaye kauyen. An ji harbe-harben bindiga amma ba a tabbatar da asarar rayuka ba.”

Wani mazaunin ya bayyana cewa, “Sun shiga Magama da safe kafin su isa Yangale inda suka yi garkuwa da mutane huɗu. Muna cikin daji da mata da yara. Don Allah ku taya mu da addu’a, muna bukatar taimako.”

A ranar Asabar, sama da ’yan bindiga 100 sun kutsa garin Talle a yankin Kulho na Karamar Hukumar Mashegu.

Mazauna sun ce maharan sun iso kauyen da misalin ƙarfe 2 na rana, suka umarci masu shaguna su rufe. Sun kuma toshe duk hanyoyin shiga da fita daga garin, sai kaɗan da suka yi nasarar guduwa.

Hakazalika, mazauna Ragada da wasu kauyuka a Mariga sun bar gidajensu tun ranar Lahadi saboda motsin ’yan bindiga a yankin.

Wani daga cikinsu ya ce, “Mun kwana a kan duwatsu duk da ruwan sama, yayin da muna kallo ’yan bindiga suna dafa abinci a gidajenmu.”

A ranar Asabar da rana kuma, an yi garkuwa da matafiya da dama a kan hanyar Kontagora–Rijau.

Martanin ’yan sanda

Kakakin rundunar ’yan sanda ta Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da harin da aka kai a hanyar Ibbi–New Bussa.

Ya ce wani ɗan sanda ya ji rauni, sannan motar sintirin ’yan sanda ta lalace yayin musayar wuta da ’yan bindigar.

Ya ce: “A ranar 29 ga Satumba, 2025, da ƙarfe 11:30 na safe, wasu ’yan bindiga suka kai hari a wurin sintirin ’yan sanda a kan hanyar Ibbi–Bussa.

“Jami’an sintirin sun yi nasarar mayar da martani, amma motar sintirin ta samu rauni, sannan ɗaya daga cikin ’yan sanda ya ji harbin bindiga kuma aka kai shi asibiti

Ya ƙara da cewa: “Abin takaici, ’yan bindigar da suka tsere daga wurin sun toshe hanyar a gaba, suka yi awon gaba da fasinjoji daga akalla motoci uku.

“Rundunar ta tura ƙarin jami’an sintiri tare da hadin gwiwar sauran jami’an tsaro da sa-kai domin bin sawun masu garkuwa da nufin ceto mutanen da aka sace da kuma kama maharan.”


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *