Shugaban Kasar Sin Ya Tattauna Da Takwaransa Na Kasar Uruguay


A yau Talata da safe, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tattauna da takwaransa na kasar Uruguay, Yamandu Orsi a nan birnin Beijing.

A yayin tattaunawar, shugaba Xi ya ce, har kullum Sin da Uruguay na martaba juna da kuma aiwatar da hadin gwiwar cin moriyar juna, kuma kasashen biyu za su ci gaba da zurfafa huldar abota bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni. Sin na goyon bayan Uruguay wajen zama kasar dake karbar shugabancin kwarya-kwarya na “kungiyar G77 da kasar Sin”, haka kuma tana son hada hannu da Uruguay wajen tabbatar da bunkasar mabambanta kasashe da dunkulewar tattalin arzikin duniya, don gina al’ummar Sin da kasashen Latin Amurka mai kyakkyawar makoma ta bai daya.

Shugaba Orsi a nasa bangaren ya ce, manufar kasar Uruguay ce ta raya hulda da kasar Sin, kuma kasarsa na tsayawa tsayin daka a kan bin ka’idar Sin daya tak a duniya, haka kuma kasar na son zurfafa hadin gwiwarta da kasar Sin ta fannoni daban daban, don kiyaye cudanyar mabambantan bangarori da kuma moriyar kasashe masu tasowa.

Bayan tattaunawar, kasashen biyu sun daddale yarjejeniyoyin hadin gwiwa sama da 10, kuma shugabannin biyu sun hallara a wajen. (Lubabatu Lei)



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *