Ba Za A Iya Daidaita Batun Mashigin Hormuz Ba Har Sai An Kawo Karshen Yaki
[ad_1]
Ministan ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya ce kalubalen zirga-zirga ta mashigin Hormuz, sakamako ne na tashin hankali da ake ciki yanzu haka, kuma ba za a iya daidaita batun mashigin ba har sai an kawo karshen yaki.
Wang, wanda memba ne a ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, ya bayyana hakan ne a jiya Alhamis, yayin tattauna ta wayar tarho tare da takwaransa na Saudiyya Faisal bin Farhan Al Saud.
A nasa bangare Farhan Al Saud, cewa ya yi Saudiyya na dora muhimmancin gaske kan muhimmiyar rawar da Sin ke takawa a harkokin kasa da kasa, kana tana martaba hadin gwiwar koli bisa manyan tsare tsare tsakaninta da Sin. Kazalika, Saudiyya a shirye take ta zurfafa tuntuba, da tsare-tsare tare da Sin karkashin dandaloli daban daban ciki har da MDD, ta yadda za su ingiza matakan sassauta yanayin da ake ciki da kuma kawo karshen yaki baki daya.
Har ila yau, a dai jiyan, Wang Yi ya zanta ta wayar tarho tare da takwaransa na Jamus Johann Wadephul, inda ya bayyana muhimmancin martaba ikon mulkin kai da tsaron kasashen yankin Gulf. Yana mai cewa, wajibi ne a samar da kariya ga fararen hula, da sauran wurare da ba na ayyukan soji ba. Kazalika, ya zama wajibi a kare hanyoyin zirga-zirgar jiragen ruwa, da albarkatu da cibiyoyin sarrafa makamashi.
Bugu da kari, Wang ya zanta ta wayar tarho da babbar wakiliyar hukumar gudanarwar tarayyar Turai a fannin harkokin waje da manufofin tsaro Kaja Kallas, inda ya shaida mata cewa, wajibi ne matakan kwamitin tsaron MDD su zamo wadanda ba za su samar da kariyar doka ga duk wasu haramtattun matakan soji, ko ruruta yanayin da ake ciki, ko kara tsananta tashin hankali ba. (Saminu Alhassan)
[ad_2]
Source link