Mutum ɗaya ya rasu yayin da ’yan sanda da ’yan bindiga suka yi artabu a Kwara

[ad_1]



An kashe wani da ake zargin ɗan bindiga ne, yayin wani artabu da ’yan sanda da ’yan sa-kai suka yi da wasu mahara a Jihar Kwara.

Lamarin ya faru ne a ƙauyen Adekanbi, kusa da garin Bode Saadu.

Rahotanni sun nuna cewa ’yan bindigar sun yada zango a saman wani dutse da ke kallon ƙauyen.

Suna hangar jami’an tsaro sai suka fara harbi ba ƙaƙƙautawa.

’Yan sanda da jami’an sa-kai sun yi artabu tare da tarwatsa maharan, inda wasu daga cikinsu suka tsere da raunin harbin bindiga.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Adetoun Ejire Adeyemi, ta tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ta fitar ranar Juma’a.

Bayan an artabun, jami’an tsaro sun duba yankin, inda suka samu gawar mutum ɗaya da ake zargin ɗan bindiga ne.

Haka kuma an gano bindiga ƙirar AK-49 da harsasai 32 a wajen.

SP Adetoun, ta ce wannan aikin wani muhimmin ci gaba ne a ƙoƙarin da rundunar ke yi wajen kawar da masu aikata laifi a jihar.

Ta kuma roƙi jama’a da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai a kan lokaci domin taimaka wa yaƙi da laifuka.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *