Gwamnati ta kare shirin aiwatarwa a watan Janairu
[ad_1]
Gwamnatin Tarayya ta kare shirinta na fara aiwatar da sabbin dokokin haraji daga watan Janairu 2026.
Fadar Shugaban Ƙasa ta fuskanci suka daga jama’a kan zargin sauya wasu sassa da bambance-bambancen da ke tsakanin dokokin da Majalisar Dokoki ta amince da su da kuma wanda aka wallafa a kundin gwamnati.
Shugaban Kwamitin Shugaban Kasa kan Manufofin Kkuɗi da Sauye-sauyen haraji, ya yi gargadi cewa jinkirta aiwatar da sauye-sauyen zai iya ƙara tsadar kayan masarufi da ayyuka, ciki har da abinci, kiwon lafiya da ilimi, tare da ci gaba da ɗora wa ma’aikata da kananan ’yan kasuwa nauyin haraji mai yawa.
Oyedele, a wata hira da aka yi da shi a tashar Channels TV a ranar Litinin, ya ce adawa da sauye-sauyen ba da zargin sauya dokokin ta fara ne , saboda tun kafin rikicin ya fara akwai masu kira da a dakatar da shirin.
Ya danganta adawar da yaƙi da sauye-sauyen da yaɗa bayanan da ba su da tushe, yana mai jaddada cewa ikon dakatarwa ko jinkirta aiwatar da dokokin na hannun Majalisar Dokoki.
A cewarsa, “Ko kafin batun sauya dokokin ya taso, akwai masu kira da a dakatar da shirin saboda dalilai daban-daban. Babban matsalar da muke fama da ita ita ce yaɗa bayanan da ba su da tushe,” in ji shi.
Ya ce jinkiri zai sa a ci gaba da amfani da tsarin haraji na yanzu wanda ke ɗora wa ma’aikata da ƙananan kasuwanci nauyi mai tsanani.
A cewarsa, kashi 98 cikin 100 na ma’aikata za su ci gaba da biyan haraji fiye da kima, yayin da ƙananan kasuwanci za su ci gaba da rasa rangwame kuma su fuskanci haraji da yawa.
Oyedele ya ƙara da cewa manyan kamfanoni za su ci gaba da fama da haraji marasa amfani, yayin da harajin ƙaramar riba zai ci gaba da shafar masu ƙaramin albashi da kasuwancin da ba su da riba.
Haka kuma, harajin ƙarin ƙima da aka ɓoye zai ci gaba da ƙara tsadar abinci, kiwon lafiya da ilimi.
Ya ce: “Illar jinkiri shi ne za aci gaba da tsarin da ake kai yanzu — ma’aikata suna biyan haraji fiye da kima, ƙananan kasuwanci suna rasa rangwame, manyan kamfanoni suna fama da haraji marasa amfani, kuma harajin ƙaramar riba da VAT da aka ɓoye suna ƙara tsadar kayan masarufi da ayyuka. Wannan yana nufin tattalin arziki zai ci gaba da gurɓata.”
Kan zargin sauya wasu sassa na dokokin bayan Majalisar Dokoki ta amince da su, Oyedele ya ce ko da an tabbatar da hakan, abin da ya dace shi ne a ware waɗannan sassan a ɗauke su a matsayin ba su cikin doka.
Ya ce, “Za a iya aiwatar da dokar kamar yadda Majalisar Dokoki ta amince da ita, sannan a binciki yadda waɗannan sassan suka shiga da abin da ya kamata a yi da su.”
Ya bayyana cewa kwamitinsa ya riga ya gano wasu wurare a cikin dokokin da Majalisar ta amince da su da ke buƙatar gyara, ciki har da batun ma’anoni da ambato.
“Misali, an bayyana ƙananan kasuwanci ta hanyoyi biyu daban a cikin sabbin dokokin. Ya kamata a yi amfani da ma’ana ɗaya don kada jama’a su rikice. Waɗannan matsalolin suna buƙatar gyara daga ’yan majalisa,” in ji shi.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link