Ingantaccen Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Wa Duk Duniya Nagartattun Damammaki

[ad_1]

Gwamnatin Sin ta bayyana karuwar tattalin arzikin kasar da kaso 5 cikin 100 a shekara ta 2025 jiya Litinin, inda kafofin yada labarai na kasa da kasa suka bayyana ci gaban Sin a matsayin “ci gaban da ya wuce tsammani” kuma mai “karfin juriya”.

Ci gaban da Sin take samu a wannan karo ya kasance ingantacciyar bunkasuwa a bisa halin da ake ciki a duniya. Shekara ta 2025 ita ce shekarar kammala shirin bunkasa ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’ummar Sin na shakaru biyar-biyar karo na 14, inda GDPn kasar ta fara wuce Yuan tiriliyan 140, kuma an cimma nasarar manyan manufofin ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’umma. Wannan ba wai kawai yana nufin nasara a shirin na 14 ba ne, har ma ya kafa ginshigi mai karfi don kyakkyawan fara shirin karo na 15. Idan aka kwatanta da sauran kasashe, saurin ci gaban tattalin arzikin Sin ya kasance a sahun gaba a duniya, ya zama karfin ingiza ci gaban tattalin arzikin duniya mafi kwanciyar hankali kuma mafi dogaro, yawan gudunmawar da Sin za ta bayar ga ci gaban tattalin arzikin duniya da aka yi hasashe zai kai kashi 30 cikin 100 .

Abin da ya dace a ambata shi ne karfin “juriya” na tattalin arzikin Sin, wanda ke ba da ingantaccen tabbaci ga tattalin arzikin duniya dake fuskantar halaye masu sarkakiya. Kafofin waje kamar CNBC sun nuna cewa, samun irin wannan sakamako ya kasance mai wahala ga tattalin arzikin Sin, duba da matsin lamba na yakin haraji da ya lalata tsarin cinikayyar duniya da kuma karuwar rashin tabbas.

A halin yanzu, akwai tashin hankalin siyasar duniya da yadda manufar kariyar cinikayya ke kara kunno kai, kana yanayin duniya na ci gaba da zama mai sarkakiya. Amma duk da haka, ginshigin tattalin arzikin Sin ba zai canja ba, yayin da fa’idodin ci gaba za su kara bayyana a lokacin shirin bunkasa ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’ummar Sin na shakaru biyar-biyar karo na 15. Karfin juriya da tattalin arzikin Sin ya nuna da kuma azamar gwamnatin Sin ta ci gaba da bude kasuwa da kofarta, sun bayar da sako ga duniya cewa, ba shakka, Sin za ta ci gaba da taka rawar gani ga ci gaban tattalin arzikin duniya da krikire-kirkire. (Amina Xu)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *