Matar Da Ta Haifi ‘Ya’ya Hudu Lokaci Guda Na Tsaka Mai Wuya A Kano
[ad_1]
Malama Aisha Abubakar, wacce Ubangiji ya azurtata da haihuwar ‘ya’ya hudu rigis a Jihar Kano da aka sauya wa suna Halima, Fatima, Abubakar, Bilal tana tsaka mai wuya sakamakon karancin abin hannu na maigidanta, ya sa matar na cikin tsananin bukatar taimako daga gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf da Sarkin Kano, da manyan attajiran Kano irinsu, Alhaji Aliko Dangote da Alhaji Abdussamad Isyaka Rabiu, wadanda suka yi suna wajen tallafawa raunana a ciki al’umma.
Matar ce wanna haihuwa ita ce haihuwarta ta shida kuma ta biyu a yin ta gwaye kafin wannan haihuwar ‘ya’ya hudu a lokaci guda.
- Gobara Ta Hallaka Mutum 2, Ta Lalata Dukiya Ta Biliyan 1.59 A Bauchi
- An Haska Fim Na Yayata Shirin CMG A Liyafar Murnar Sabuwar Shekara Ta Ofishin Jakadancin Sin A Kasar Holland
Ta ce yanzu haka kasa da wata hudu jariran nan hudu sun sha madara ta sama da miliyan biyu, wanda rashin kudi ya sa maigidanta ya sai da gidansa da suke zaune, domin siya wa jariran nan hudu madara.
A karshe, ta yaba wa sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sunusi Ii kan jagoranci da ya yi musu na zuwa ganin sakataran gwamnatin Jihar Kano, inda ya yi alkawarin taimaka musu tun a wancan lokacin amma dai har yanzu lokacin rubata wannan rahotan alkawarin bai cika ba.
[ad_2]
Source link