Majalisar Kano Na Tattauna Batun Fara Amfani Da Harshen Hausa A Wurin Koyarwa A Makarantu
[ad_1]
Majalisar Dokokin Jihar Kano ta fara tattaunawa kan wani kudiri da ke neman harshen Hausa ya maye gurbin turanci wurin koyarwa a hukumance a makarantu a fadin jihar.
Musa Kachako, wanda ke wakiltar Mazabar Takai a karkashin Jam’iyyar NNPP ne ya dauki nauyin kudirin.
Da yake gabatar da kudirin a zaman majalisar, Kachako ya ce wannan kudiri an yi shi ne don karfafa tushen ilimi na dalibai da kuma daidaita tsarin ilimin Kano kamar yadda wasu manyan kasashen duniya suka yi kuma sun samu sakamako mai kyau.
Ya lura cewa kasashe kamar China, Japan, da Indiya sun cimma gagarumin ci gaba a fannin kimiyya da fasaha ta hanyar amfani da harsunan asali don koyarwa a matakin ilimi na farko.
A cewarsa, koyarwa a cikin harshen Hausa zai inganta fahimta tsakanin dalibai, rage yawan faduwa, da kuma rage yawan wadanda ake kora daga makaranta sakamakon faduwa a jarrabawa.
Bayan tattaunawa, shugaban majalisar Jibrin Ismail Falgore, ya mika kudirin dokar ga kwamitin majalisar mai kula da harkokin ilimi domin ci gaba da bincike da neman shawarwari.
[ad_2]
Source link