Yaki Bai Dace Da Moriyar Kowane Bangare Ba

[ad_1]

Shugaban kasar Amurka, ya ce za a jinkirta kai hari kan cibiyoyin wutar lantarki na kasar Iran, kana gwamnatinsa tana gudanar da shawarwari tare da jami’an kasar Iran amma ba a san sunansu ba. Game da hakan, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau Talata, cewa yaki bai dace da moriyar kowane bangare ba, kuma tsagaita bude wuta, da gudanar da shawarwari ne hanya daya tilo ta warware rikicin.

Ban da wannan kuma, Lin Jian ya bayyana cewa, wani mutum da ya bayyana kansa a matsayin jami’in rundunar ba da kariya ga Japan, ya shiga ofishin jakadancin Sin dake kasar Japan ba tare da samun izni ba, wanda Sin ba ta ji dadin hakan ba, kana ta riga ta tuntubi bangaren kasar Japan, tare da bayyana adawarta ga aukuwar lamarin. (Zainab Zhang)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *