NPC Ta Yi Rajistar Haihuwa 36,000 A Kano Cikin Watanni 9

[ad_1]

Hukumar Kididdiga ta Kasa (NPC) ta ce ta yi rijistar haihuwar yara sama da 36,000 a Jihar Kano cikin watanni tara bayan ƙaddamar da tsarin rijistar haihuwa ta intanet.

Daraktan NPC na jihar Kano, Balarabe Kabir, ya bayyana hakan yayin wani taron horar da masu horaswa na kwana biyu da aka gudanar a Kano.

An shirya taron horon ne ta haɗin gwiwar NPC da Kungiyar Shugabannin Kananan Hukumomi ta Kasa (ALGON) da kuma Hukumar Tattara Bayanan ‘Yan Kasa (NIMC), tare da tallafin Gwamnatin Netherlands ta hannun Kwammitin Majalisar Dinkin Duniya mai Kula da Asusun Kananan Yara.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *