Sace ɗalibai: Tinubu ya bai wa Ministan Tsaro umarnin tarewa a Kebbi
[ad_1]
Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya umarci Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, da ya koma jihar Kebbi da aiki sakamakon sace ɗalibai ’yan mata 25 da wasu ’yan bindiga suka yi a jihar.
Tinubu ya umurci Matawalle, wanda tsohon Gwamnan Jihar Zamfara ne, da ya zauna a Kebbi domin sa ido kan dukkan matakan tsaro da ake ɗauka domin kuɓutar da ɗaliban da aka sace.
’Yan bindiga sun sace ɗalibai 25 a Makarantar Sakandiren Mata da ke garin Maga na Jihar Kebbi da misalin ƙarfe 4 na Asubahin ranar Litinin.
A cewar mai magana da yawun fadar shugaban ƙasa, Bayo Onanuga wanda ya bayyana umarnin a cikin wata sanarwa da yammacin Alhamis, ana sa ran Matawalle zai isa Birnin Kebbi da safiyar Juma’a.
“Yana da ƙwarewa sosai wajen fuskantar ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane a lokacin da yake gwamnan Jihar Zamfara daga 2019 zuwa 2023,” in ji sanarwar.
“A ranar 26 ga watan Fabrairu, 2021, ’yan bindiga sun yi garkuwa da dalibai mata 279 masu shekaru tsakanin 10 da 17 a makarantar kwana ta GGSSS Jangebe, Jihar Zamfara. ’Yan bindigar sun saki dukkan waɗanda suka yi garkuwar da su a ranar 2 ga watan Maris, 2021.”
Idan za a iya tunawa, Shugaba Tinubu ya dage tafiyarsa da aka tsara zuwa Johannesburg, Afirka ta Kudu, da Luanda a kasar Angola, domin ya jira ƙarin rahotannin tsaro kan satar daliban na Kebbi da kuma harin da aka kai wa masu ibada a cocin Eruku da ke jihar Kwara.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link