’Yan bindigar da suka sace masu ibada a cocin Kwara sun nemi a ba su N3bn kafin sakin su

[ad_1]



’Yan bindigar da suka yi garkuwa da masu ibada a cocin Christ Apostolic Church da ke Eruku, a jihar Kwara, sun nemi Naira miliyan 100 a matsayin kudin fansar kowanne mutum da suka kama.

A cewar Faston cocin, Lawrence Bamidele, tsakanin mutane 30 zuwa 35 aka yi garkuwa da su a daren Talata lokacin da aka kai musu mummunan hari suna tsaka da ibada a cocin.

Majiyoyi daga iyalai da shugabannin al’umma sun tabbatar a ranar Alhamis cewa masu garkuwar sun fara kiran ’yan uwan waɗanda aka sace ta hanyar amfani da wayoyinsu.

Sakataren cocin, Josiah Agbabiaka, ya ce tuni aka fara tuntubar wasu daga cikin dangin wadanda aka sace din.

Ya ce, “Gaskiya ne cewa ’yan bindigar sun fara kiran ’yan uwa ta amfani da wayoyin waɗanda aka sace don neman kudin fansa,” in ji Agbabiaka.
“Abin da aka shaida mana shi ne sun raba waɗanda aka sace gida-gida. Rukunin farko na mutane 11 an nemi su biya Naira miliyan 100 kowanne.”

Basaraken gargajiya na yankin, Olori Eta, Cif Olusegun Olukotun, wanda ’yan uwansa huɗu na cikin waɗanda aka sace, ya tabbatar da lamarin, yana mai cewa masu garkuwar suna kiran dangin wadanda aka sace daya bayan daya.

“’Yan bindigar sun fara kiran wasu suna neman Naira miliyan 100 kan kowanne mutum. Sun ce sun raba waɗanda aka sace gida-gida, kuma suna kiran danginsu,” in ji shi.

Olukotun ya ce yana cikin cocin tare da ’yan uwansa biyar lokacin harin, inda ya ce ya tsere ta taga yayin da sauran aka tafi da su.

Jami’ar hulɗa da jama’a ta rundunar ’yan sanda ta Jihar Kwara, SP Adetoun Ejire-Adeyemi, ta ce rundunar ba ta samu wani rahoto a hukumance ba kan neman kudin fansar.

“Ba mu da masaniya kan wani neman kudin fansa ko tuntubar iyalan waɗanda aka sace,” in ji ta a ranar Alhamis.
“Dakarunmu na musamman tare da sojoji da sauran jami’an tsaro suna kan aiki don ceto waɗanda aka yi garkuwar da su.”

Ejire-Adeyemi ta ƙara da cewa Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Adekimi Ojo, ya roƙi al’umma da iyalan waɗanda aka sace da su bayar da bayanan da za su taimaka wa jami’an tsaro wajen aikin ceto mutanen kuma a kan lokaci.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *