An kashe masu garkuwa da mutane da ƙwato makamai a Filato

[ad_1]



Dakarun sojojin rundunar haɗin gwiwa ta 3 Division/Joint Task Force Operation Enduring Peace (JTF) sun kai samame maɓoyar masu garkuwa da mutane a jihar Filato.

Inda suka kashe waɗanda ake zargin tare da ƙwato makamai a wani samame da suka yi cikin gaggawa bisa samun sahihan bayanan sirri.

Samamen da aka gudanar a ranar Talata, 6 ga watan Janairu, 2026, wanda aka yi a wani wuri kusa da ƙauyen Lantom a gundumar Kadarko ta Ƙaramar hukumar Wase a wani mataki na daƙile ayyukan garkuwa da mutane da fashi da makami a yankin.

A wata sanarwa da muƙaddashin jami’in yaɗa labaran rundunar sojojin JTF Operation Enduring Peace, Kyaftin Joshua Atu John ya fitar, ya tabbatar da cewa an kama wasu mutane huɗu da farko, yayin da aka ƙwato makamai da suka haɗa da bindigogi ƙirar gida, gatari da kuma adda.

“Bincike na farko ya nuna cewa, waɗanda ake zargin suna da hannu a cikin laifukan baya-bayan nan a gundumar,” in ji shi, ya ƙara da cewa masu laifin biyu sun tsere da bindiga ƙirar AK-47.

Kyaftin John ya lura da cewa, waɗanda ake zargin sun haɗa kai da sojoji ta hanyar bayyana inda suke ɓoye makamai da alburusai a wajen garin Kadarko.

“Duk da haka, a ƙoƙarin tserewa, waɗanda ake zargin sun yi ƙoƙarin ƙwace makamin ɗaya daga cikin sojojin yayin da suke jagorantar sojoji zuwa ma’ajiyar,” in ji shi. “An dai tarwatsa su.”

Ya ƙara da cewa, ana ci gaba da gudanar da bincike domin kamo  mambobin da suka gudu tare da ƙwato bindigar da ta ɓace.

Da yake tsokaci game da samamen, babban kwamandan runduna ta 3 ta Najeriya kuma kwamandan rundunar JTF Operation Enduring Peace, Manjo Janar EF Oyinlola, ya yaba wa sojojin bisa ƙwazon da suka nuna.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *