Babakeren Amurka: Munafunci Dodo Ya Kan Ci Mai Shi

[ad_1]

A ranar Talata, shafin yanar gizo na Africa Check ya watsa wani bayani, inda ya ce, wani labarin dake yaduwa a shafukan sada zumunta, cewa “Sojojin Amurka sun kai hari kan fadar shugabancin kasar Najeriya”, karya ne.

To, duk da cewa wannan labari karya ne, yaduwarsa ta nuna damuwar da mutane suke da ita a zuci. Da ma harin da aka kai kasar Venezuela a farkon watan da muke ciki ya riga ya nuna yadda kasar Amurka take wuce gona da iri, yayin da take cin zarafin sauran kasashe. Sai dai daga bisani kasar ta sake yin barazanar kai hare-hare ga dimbin kasashe dake nahiyoyin Asiya da Turai da Latin Amurka. Har ma shugaban kasar Donald Trump ya ce dokokin kasa da kasa ba su da tasiri a kansa. Wadannan abubuwa tabbas za su jefa mutanen duniya cikin damuwa, saboda sun san cewa tun da “yau an kai hari ga kasar Venezuela, to gobe ma za a iya tasam ma wata kasa ta daban.”

Hakika barazanar da kasar Amurka ta yi abu ne mai ban tsoro. Amma tsoron ya kan ragu, idan an yi tunanin yanayin da kasar ke ciki. Sanin kowa ne, a yawancin lokuta, idan aka dubi wata dabba da ke matukar haushi, da kokarin cizon mutane, za a ga dabba ce da ta fada cikin tarko.

Idan mun waiwayi matakan soja da kasar Amurka ta dauka a wadannan watanni, misali yadda kasar ta kai hari kan na’urorin tace sinadaran Uranium na kasar Iran, da kutsa kai cikin kasar Venezuela, da yadda ta kai hari daga sama a kasar Najeriya, bayan da ta tilasta wa gwamnatin Najeriya yarda da hakan, to, za mu ga kusan duk matakai ne na gajeren lokaci. Niyyar kasar Amurka ita ce, a magance wani babban yaki da ya dade, sannan a yi kokarin samar da tasiri a duniya, don nuna ma mutanen duniya cewa “Har yanzu kasar Amurka tana da karfin yin babakere”. Amma ainihin yanayin da kasar ke ciki shi ne, tana fuskantar matsaloli a fannonin sabunta jiragen yaki na ruwa da na sama, da yunkurinta na farfado da masana’antu. Kana kasar ta fara rasa fifiko a dimbin fannonin kimiyya da fasaha. Yayin da sakamakon yakin ciniki da na fasaha da aka yi a shekarar 2025 ya nuna cewa, kasar Amurka ta riga ta rasa karfin kiyaye wani matsayi na babakere a duniya.

Dalilin da ya sa kasar Amurka ke son ci gaba da aiwatar da mulkin danniya, shi ne domin wani tsohon tunanin al’ummar yammacin duniya, wato yarda da manufar kashin dankali, da kuma “Bar mai cin nasara a wata takara ya mallaki kome”. A ganin masu nazarin huldar kasa da kasa na kasashen yamma, ba za a iya samun kwanciyar hankali a duniya ba, idan babu wata kasa da ta rike matsayi na babakere, wadda take ba da umarni domin sauran kasashe su bi.

Sai dai a wannan zamanin da muke ciki na samun bunkasar tattalin arzikin dimbin kasashe masu tasowa cikin matukar sauri, yawancin kasashe sun riga sun yi watsi da wannan tunani maras gaskiya na kasashen yamma. Wani misalin da zai iya zama shaidar hakan, shi ne, bayan da kasar Sin ta gabatar da shawarar inganta jagorancin duniya a watan Saumban bara, wadda ta jaddada muhimmancin daidaiton ikon mulkin kai na mabambantan kasashe, da kula da al’amuran duniya bisa doka, da yarda da kasancewar dimbin bangarori masu fada-a-ji a duniya, da mai da moriyar al’umma a gaban kome, da manufar daukar hakikanan matakai, zuwa yanzu shawarar ta riga ta samu goyon baya daga kasashe fiye da 150. Ban da haka, kasar Sin ita ma ta gabatar da ra’ayinta, wanda shi ma ya kasance na galibin kasashe, wajen tarukan kasa da kasa daban daban, inda ta ce: Ya kamata a daidaita huldar kasa da kasa bisa ka’idoji, maimakon barin wasu kasashe su ci gaba da yin kashin dankali. A zamanin da muke ciki, mulkin danniya ba zai samu nasara ba. Kana ya kamata manyan kasashe su zama wadanda suka fara bin doka da ka’ida.

Hakika, abin da mai aiwatar da mulkin danniya bai fahimta ba shi ne, ta karfin tuwo za a iya kwatar albarkatu da dukiya, amma ba za a iya samun amincewar jama’a ba. Kana matakin tsoratar da saura ba zai taba haifar da kauna da sahihanci ba. Yanzu mun ga yadda wata kasa ta kama hanyar faduwa, amma tana ci gaba da cin zarafin sauran kasashe, da kwace albarkatu yadda ta ga dama, amma sanin kowa ne, “munafunci dodo ne ya kan ci mai shi”. (Bello Wang)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *