Kotun Koli Ta Yi Watsi Da Ƙarar Kisan Kudirat Abiola, Ta Sallami Al-Mustapha

[ad_1]

Kotun Koli ta Nijeriya, a ranar Alhamis, ta yi watsi da ƙarar da Jihar Legas ta shigar kan tsohon Babban Jami’in Tsaro na tsohon shugaban mulkin soja, Major Hamza Al-Mustapha (mai ritaya), game da kisan Alhaja Kudirat Abiola, matar wanda ake hasashen shi ne ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na 1993, marigayi M.K.O. Abiola. An kashe Kudirat Abiola ne a Legas a lokacin zanga-zangar da ta biyo bayan soke sakamakon zaɓen.

Al-Mustapha, wanda ya taɓa zama Chief Security Officer (CSO) ga marigayi Janar Sani Abacha, an zarge shi da hannu a kisan, tare da Mohammed Abacha da Lateef Shofolahan. An gurfanar da su a gaban Babbar Kotun Jihar Legas kan tuhume-tuhume biyu da suka shafi haɗin kai wajen aikata kisa da kuma kisan Kudirat Abiola a ranar 4 ga Yuni, 1996.

  • Kwamitin Binciken Tallafin Mai Na Tsare-tsaren Neman Mafita – Hon. Almustapha
  • Zamfara: PDP Ta Yaba Wa Kotun Abuja Kan Nasarar Da Ta Samu

A ranar 30 ga Janairu, 2012, Babbar Kotun Legas ƙarƙashin Mai Shari’a Moji Dada ta same su da laifi tare da yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya. Sai dai Kotun Ɗaukaka Ƙara, a ranar 12 ga Yuli, 2013, ta soke wannan hukunci, ta sallame su gaba ɗaya bisa hujjar cewa ɓangaren masu gabatar da ƙara bai gabatar da hujjojin da suka isa yanke hukunci ba.

Daga bisani, Jihar Legas ta garzaya Kotun Ƙoli don ƙalubalantar hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara, inda ta nemi a dawo da hukuncin kisa. A shekarar 2014, Kotun Koli ta ba jihar izinin sake buɗe ƙarar, duk da cewa lokacin shigar da ƙara ya wuce. Sai dai a zaman da aka yi a wannan mako, jihar ba ta aiko da lauya ko kuma ta gabatar da wata takarda ba tun daga lokacin da aka ba ta izinin ba

A hukuncin da wani kwamitin alƙalai biyar ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Uwani Aba-Aji ta yanke, Kotun Ƙolin ta ce Jihar Legas ta nuna rashin sha’awar ci gaba da shari’ar. Kotun ta jaddada cewa shekaru tara sun isa a shigar da ƙarar, don haka ta yi watsi da shari’ar gaba ɗaya, tare da tabbatar da sallamar Al-Mustapha.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *