An kashe masu haƙar ma’adinai 7 a Filato
[ad_1]
A wani ƙazamin harin da aka kai a wani wurin haƙar ma’adinai a yankin Kuru, Qaramar hukumar Jos ta Kudu a jihar Filato, ya yi sanadin mutuwar mutane bakwai.
An gano cewa harin wanda ya auku a daren ranar Laraba, ya kuma jikkata wasu.
Babban mataimaki na musamman ga Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang kan harkokin ma’adinai, Emmanuel Solomon ne ya tabbatar da kai harin kamar yadda majiyar PUNCH ta ruwaito a Jos ranar Alhamis.
Solomon ya ce, “Yanzu an sanar da ni labarin harin da aka kai a yankin Kuru wanda ya faru ranar Laraba da daddare, mutum bakwai ne suka mutu a harin. Kuma ina hanyar gani da ido zuwa inda lamarin ya faru.
Da yake bayyana lamarin a matsayin “abin takaici,” ya lura cewa hakan ya biyo bayan cin zarafin da ake yi wa masu haƙar ma’adinai a yankin Qaramar hukumar.
“Kafin ranar Laraba , a wata unguwa a Gyel, maharan sun far wa mutane uku, amma ɗaya daga cikinsu ya tsere, sai dai abin takaici, biyu sun mutu, waɗanda abin ya rutsa da su suna kan hanyarsu ta zuwa wani wurin haƙar ma’adinai ne aka yi musu kwanton ɓauna aka kashe su,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa, makonni biyu da suka gabata wasu ‘yan bindiga sun yi wa wani gungun masu haƙar ma’adinan kwanton ɓauna, inda suka kashe biyu tare da raunata ɗaya.
“Wanda ya samu rauni a halin yanzu yana asibitin Lome yana samun kulawa, kuma wanda ya mutu ƙanina ne, abin takaici ne yadda wasu ke yunƙurin kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba a jihar,” kamar yadda Solomon ya bayyana, muryarsa cike da baƙin ciki.
Solomon ya jaddada cewa lamarin “yana buƙatar kulawar gaggawa” kuma ya yi alƙawarin cewa gwamnatin jihar za ta ” duba lamarin domin masu haƙar ma’adinai su sami tallafin tsaro a nan gaba.”
Da aka tuntuɓi Kwamandan hukumar kula da dazuzzukan na yankin Jos ta Kudu, Pam Gyang Pwajok, ya musanta labarin faruwar lamarin.
Sai ya ce “Bari in gano abin da ya faru, zan dawo gare ku”, in ji shi.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link