Roberto De Zerbi Ya Raba Gari Da Olympique Marseille
[ad_1]
Kocin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Marseille ta ƙasar Faransa, Roberto de Zerbi ya bayyana ajiye aikinsa na horar da kungiyar.
Hakan na zuwa ne bayan da PSG ta lallasa Marseille da ci 5-0 tare da ficewa daga gasar zakarun Turai bayan shan kashi a hannun Club Brugge da ci 3-0.
- Yadda Amurka Za Ta Iya Yin Tasiri A Zaɓen Nijeriya Na 2027 — Yakubu Dogara
- Ofishin Jakadancin Sin A Mozambique Ya Shirya Liyafar Murnar Bikin Bazara
De Zerbi ya karɓi ragamar horas da Marseille a shekarar 2024 bayan ya bar Brighton, inda ya shafe ƙasa da shekaru biyu yana jagorantar ƙungiyar ta ƙasar Faransa.
De Zerbi ya jagoranci ƙungiyar ta Marseille zuwa matsayi na biyu a gasar Ligue 1 a kakar wasa da ta gabata, yanzu haka ƙungiyar na matsayi na huɗu a gasar Ligue 1.
A cikin sanarwar da ƙungiyar ta fitar ta bayyana cewar ɓangarorin biyu sun raba gari bayan cimma yarjejeniya a tsakaninsu, inda tace “Olympique de Marseille da Roberto De Zerbi, kocin tawagar farko, sun sanar da kawo ƙarshen yarjejeniyarsu”, in ji Marseille a cikin sanarwar.
[ad_2]
Source link