Kuri’un Jin Ra’ayin Al’ummun Kasa Da Kasa Sun Kara Jaddada Amincewa Da Kasar Sin


Kuri’un jin ra’ayin al’ummun kasa da kasa na mutane kusan 51,700, daga kasashe masu ci gaba 15, da kasashe masu tasowa 31, sun kara jaddada amincewar sassan kasa da kasa da kasar Sin.

Cibiyar kwararru ta “Global Times Institute” ce ta wallafa sakamakon binciken na “Global Times 2025” a Litinin din nan, dangane da mahangar duniya game da kallo, da fahimtar da ake yiwa kasar Sin.

Binciken ya bayar da damar tambayar al’ummun kasashen waje, mahangarsu game da wasu muhimman batutuwa, kamar tunanin shugaba Xi Jinping game da salon gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin a sabon zamani, mai kunshe da tunani kamar na “Gina al’umma mai makomar bai daya ga dukkanin bil’adama”, da tunanin nan na “Ruwa mai tsafta da tsaukuna masu dausayi muhimman kadarori ne”, wadanda dukkaninsu suka samu karbuwa daga kusan kaso 80 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyin. (Mai fassara: Saminu Alhassan)



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *