An kama ɗan fashi da ake zargi da ƙwato daloli na bogi

[ad_1]



Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta samu gagarumar nasara a yaqi da aikata laifuka bayan kama wani da ake zargi ɗan fashi ne, tare da ƙwato kuɗaɗen dalolin Amurka na bogi da wasu kayayyaki masu haɗari a sassa daban-daban na jihar.

A wata sanarwa da kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya fitar ya ce nasarorin sun samo asali ne ta hanyar aikin tsaro na leƙen asiri da sintiri na zamani da jami’an rundunar ke yi.

Ya bayyana cewa, jami’an ofishin ’yan sanda na Pindiga sun cafke wani mai suna Shehu Hussaini daga ƙauyen Mansur a Ƙaramar Hukumar Alkaleri ta Jihar Bauchi, a ranar 18 ga Janairu, 2026.

An kama shi ne yayin da jami’an ke sintiri na binciken ababen hawa, inda aka same shi da harsasai 13 da adda da kuma babur ƙirar Honda.

DSP Abdullahi ya ce, “Wanda ake zargin bai iya bayar da gamsasshen bayani kan kayan da aka same shi da su ba.

Binciken farko ya nuna cewa, yana kan hanyarsa ne domin kai harsasan ga shugabansa da ke ɓoye a cikin daji a yankin Mansur na Alkaleri.

A wani ɓangaren kuma, rundunar ta samu nasarar ceto Hon. Hassan Reuben daga ƙauyen Nahuta, Tula a Ƙaramar Hukumar Kaltungo.

Kakakin rundunar ya ce an sace mutumin ne a ranar 20 ga Janairu, 2026, amma washegari aka samu nasarar ceto shi ba tare da ya ji rauni ba, ta hanyar aikin haɗin gwiwa tsakanin jami’an ’yan sanda na Awak da Tula, tare da taimakon ’yan banga da mafarauta na yankin.

An ceto shi ne a Tule Berbere kusa da ƙauyen Kunge a gundumar Awak, Ƙaramar Hukumar Kaltungo.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *