Ayyukan Ta’addanci A Jihar Kano: Ina Mafita?

[ad_1]

Masu nazarin harkokin yau da kullum sun bayyana cewa, ƙaruwar ayyukan ta’addanci musamman a cikin wannan watar ta Janairu 2026 a Jihar Kano ya ta’allaƙa ne saboda wasu dalilai masu dangantaka da juna. Dalilan kuma sun haɗa daga ayyukan masu aikata laifuka a cikin unguwanni da kuma yadda aka samu watsowar vurvushin bazuwar ƴan ta’adda daga wasu yankunan ƙasar nan.

A wani hari na baya-baya nan da wasu vata gari suka shiga har cikin gida suka kashe matar aure da ƴa’yan 6, abin da ya tayar da hankulan al’umma. Haka kuma ya tsananta buƙatar neman mafita tare da kawo ƙarshewn irin waɗannan kisan babu gaira babu dalili.

  • Gwamnan Kano Ya Yi Allah-wadai Da Kisan Uwa Da ‘Ya’yanta 6, Ya Umarci A Kamo Masu Laifin
  • Kisan Gillar Mutum 7 A Kano: Sarakuna Da Malamai Da Iyaye Sun Nemi A Gaggauta Yanke Wa Waɗanda Ake Zargi Hukunci

Bayanai sun nuna cewa, faɗaɗar ayyukan ƴan ta’adda daga jihohi maƙwabta kamar Zamfara da Kaduna da Katsina ya bazu zuwa wasu ƙananan hukumomin da ke maƙwabtaka da waɗannan jihohin. Idan za a iya tuna farmakin ƴan ta’adda da ake yawaitar samu a wajajen ƙarshen shekarar 2025 a wasu ƙauyukan ƙaramar hukumar Shanono. Hare haren sun haɗa da garkuwa da mutane musamman mata da yara ƙanana da sace-sacen shanu haka kuma an samu faɗace-faɗace a tsakanin jami’an tsaro da ƴan bindigan a wasu wurare.

Wani vangare da masana suka tabbatar da suna bayar da gudummawa wajen haifar da ƙarin hare-hare da ayyukan ta’addanci a birarenmu sun haɗa da matsalolin zamantakewa na iyalai wanda yakan kai ga haifar da rikiice-rikice, misali shi ne irin harin da aka kai a unguwar Chiranci wanda ya yi sanadiyyar mutuwar matar aure da ƴa’yanta 6. Domin wanda ake zargin ya jagoranci kai harin ɗanuwa ne ga matar kuma suna fama rikici ne a tsakaninsu na abin da ya shafi rabon gado.

Haka kuma a ƴan shekarun nan Jihar Kano musamman ƙwaryar birnin ya fuskanci hare-hare da rikice-rikiice a tsakanin ƙungiyoyin ƴan daba na unguwanni irin wannan faɗace-faɗace ya fi ƙamari a ungunnin Kurna Mayanka da Tudun Fulani. A bayyane yake yadda waɗannan matasa suke yawo ɗauke da muggan makamai suna kai wa juna harin ramuwar gayya. Waɗannan matasan sune kuma suke a kan gaba wajen ƙwacen waya. Matane da dama sun rasa rayukansu a sanadiyyar hari da makami a yayin da ake ƙoƙarin ƙwace musu waya a unguwanni da dama a birnin Kano.

Duk da ƙoƙarin ƙungiyoyi irin su NDLEA da HISBA da sauran jami’an tsaro, safara da shaye-shayen muggan ƙwayoyi ya ci gaba da bunƙasa a tsakanin matasa a sassan Kano. Wannan mummunan aikin ya ratsa har cikin gidaje inda ake saman matan aure da ƴan mata suna ta’ammali da muggan ƙwayoyi. Wanda mu’amala da muggan ƙwayoyin ake yi ke ƙara ayyukan masu aikakata laifukka a tsakanin al’umma a faɗin jihar.

Xaukar doka a hannu a tsakanin matasa ya ƙara haifar da matsalolin tsaro a, a watan Mayun shekarar da ta gabata a garin Rano wasu matasa sun yi sanadiyyar mutuwar wani DPO na ƴansanda sakamakon rufe shi da duka da suka sakamakon wani savani da aka samu a tsananin su. A wasu lokutta ma ana samun hare-hare inda wasu ke ɗaukar nauyin ƴan ta’adda domin su kashe musu abokan hamayyar su.

Tabbas ana fuskantar matsalolin tsaro a Jihar Kano kamar yadda yake a yawancin jihohin ƙasar nan musamman a arewacin ƙasar nan, amma yadda ake samu bazuwar ƙananan makamai abu ne mai tayar da hankali. Dole a yaba wa jami’a tsaro a kan irin wannan nasarar da suke samu domin hakan yana daƙile ayyukan masu aikata laifi. Amma wani hanzari ba gudu ba, dole a rinƙa tabbatar an hukunta dukkan waɗanda aka kama da laifi. Hakan zai ƙarfafa wa al’umma wajen bayar da bayanan sirri ga jami’an tsaro ta yadda za a ci gaba da kama masu aikata laifukka.

Haka kuma ya kamata gwammnati ta tabbatar da an samar wa jami’an tsaronmu cikakken kayan aiki, ta yadda za su gudanar da ayyukansu na kare al’umma cikin jin daɗi. A kuma bayar da muhimmanci ga albashi da kuɗaɗen sallama da kuɗaɗen da ake ba iyalan jami’an da suka rasa rayukansu a fagen fama.

An tabbatar da cewa, matsalolin tattalin arziƙi, jahilci da tsadar rayuwa suna taimakwa wajen ƙaruwar ayyukan ta’addanci. An ƙiyasta cewa, akwai kashi 33.3 na matasanmu da suke garanramba ba tare da aikin yi ba a biranen mu wanda hakan yake ƙara zafafa ayyukan ta’addanci a tsakanin matasan.

Ya kuma kamata ƴan siyasa su gudanar da ayyukan ci gaban al’umma kamar yadda suka yi alkawari a lokuttan da suke yaƙin neman zave. Su kuma matasa ya kamata su yi wa kansu karatun ta natsu wajen ƙin yarda a yi amfani da su wajen kai hare-hare ga abokan hamayyar siyasa, musamman yanzu da aka shiga lokuttan harkokin siyasa.

ina mai yaba wa da ƙoƙarin rundunar ƴansanda Jihar Kano a kan yadda ta yi amfani da ƙwarewar ta wajen zaƙulo cikin gaggawa waɗanda suka yi kisan na Xorayi Charancci. Tabbass sun nuna ƙwarewa da kishin ƙasa da fatan hakan zai ɗore. Allah ya ci gaba da kawo mana zaman lafiya a unguwanninmu jihohinmu da ƙasar mu gaba ɗaya.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *