Ministan Harkokin Wajen Sin Zai Ziyarci Italiya Da Switzerland
[ad_1]
Daga ranar 7 zuwa 12 ga wata, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, zai ziyarci kasar Italiya tare da halartar taron hadin gwiwa na 12 na kwamitin gwamnatocin Sin da Italiya, sannan ya je kasar Switzerland don halartar taro zagaye na 4 na ministocin harkokin wajen Sin da Switzerland.
Ma’aikatar harkokin wajen Sin ce ta sanar da hakan a yau Lahadi, inda ta ce, Wang Yi wanda kuma mamba ne na ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, zai yi ziyarace-ziyarcen ne bisa gayyatar da mataimakin firaminista kuma ministan harkokin wajen Italiya Antonio Tajani da ministan harkokin wajen Switzerland Ignazio Cassis suka yi masa. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp
[ad_2]
Source link