Adadin Ikon Mallakar Fasaha A Kasar Sin Ya Kai Miliyan 5.32
[ad_1]
Hukumar kula da hakkin mallakar fasaha ta kasar Sin ta ce adadin ikon mallakar fasaha da a ke da su a babban yankin kasar Sin ya kai miliyan 5.32 ya zuwa karshen bara.
Hukumar ta kara da cewa, ta bayar da izinin mallakar fasaha 972,000 a shekarar da ta gabata, kana an rage lokacin da ake dauka na tantance bukatar samun izinin zuwa watanni 15.
Matsakaicin adadin ikon mallakar fasaha masu daraja a kasar ya kai 16 cikin mutane 10,000 a 2025.
Haka kuma, akwai sama da tamburan mallakar harkokin kasuwanci miliyan 4.2 masu rajista a babban yankin kasar Sin a bara, kuma jimilar tamburan dake da cikakken rajista ya zarce miliyan 49.87 ya zuwa 2025. (FMM)
[ad_2]
Source link