Kamfanin Shell zai zuba jarin dala biliyan 20 a Najeriya — NNPCL
Shugaban Gudanarwa na Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPCL), Mista Bashir Bayo Ojulari, ya bayyana cewa Kamfanin Shell Petroleum Development Company ya shirya tsaf don zuba jari na dala biliyan 20 a Najeriya.
Kamfanin zai zuba jarin ne a cikin shekaru biyu masu zuwa bayan sabunta ƙwarin-gwiwar masu zuba jari da gyare-gyaren Gwamnati suka haifar kwanan nan.
Ojulari wanda ya ce, hakan ya biyo bayan ƙarfafa gwiwa da sauye-sauyen gwamnati mai ci ya haifar, ya bayyana hakan ne a yayin da yake zantawa da ‘yan jarida a ranar Juma’a a fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
Ya ce, tsarin nada nasaba da umarnin aiwatar da ƙudurori da za su jawo hankalin masu zuba jari kai-tsaye daga ƙasashen ƙetare ko (FDI) a fannin Mai da iskar Gas na Najeriya, da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bada umarni a kai a shekara ta 2025.
A cewarsa, Umarnin Zartarwa, wanda aka gabatar bayan aiwatar da Dokar Masana’antar Man Fetur (PIA), an tsara su ne don havaka yin gasa wajen zuba jari a Najeriya a robaangaren makamashi.
Ya ce, “Gasar saka hannun jari ta duniya ce; kuma wasu ƙasashe na sauya manufofinsu ta hanyar da ta dace don jawo hankalin masu zuba jari.
Ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da Shugaba Tinubu ya yi shi ne gabatar da Umarnin Zartarwa (Executive Order), wanda ya ƙara wa masu zuba jari ƙwarin-gwiwa”, in ji Ojulari.
Ya bayyana cewa, bayyana manufofi da sassaucin da Gwamnatin Tarayya ta nuna sun bai wa kamfanin Shell damar kammala raba kadarorin haɗin-gwiwa na ƙasashen waje, waɗanda a ka mayar wa Kamfanin Renaissance Africa Energy Company.
Ojulari ya ce nasarar da aka samu wajen samar da sasaauci a robaangaren, ya ƙara wa ƙasashen duniya ƙwarin-gwiwa; kuma ya yi tasiri kai-tsaye kan shawarwarin saka hannun jari na Shell a Najeriya.
Shugaban kamfanin na NNPCL ya kuma ce, kamfanin Shell ya ɗauki matakin zuba jari da a ka fi sani da suna (FID) na dala biliyan 5 don haɓɓaka filin Mai na Bonga, sannan kuma ya sake zuba jari na dala biliyan 2 a wani aikin haɓɓaka iskar Gas mai zurfi wanda a ka sani da suna HI.
“A jimilla, kamfanin Shell ya zuba jari sama da dala biliyan 7 tun bayan sanar da tallafin. Za ku iya fahimtar abin da wannan ke nufi idan aka duba irin wannan ƙwarin-gwiwa ga sauran masu zuba jari”, in ji shi.
Shugaban NNPCL ya bayyana cewa a yanzu kamfanin na Shell ya tabbatar wa Shugaba Tinubu shirye-shiryen neman sabbin damar saka hannun-jari da darajarsu ta kai dala biliyan 20 a cikin shekaru masu zuwa; wanda hakan ke nuni da bunƙasar da Najeriya ta yi a robaangaren zuba jari kan makamashi.