’Yan jarida 7 sun mutu a hatsarin mota a Gombe
[ad_1]
Rahotanni sun tabbatar da cewa ma’aikata shida na Gidan talabijin na Kasa (NTA) da ke Gombe sun rasa rayukansu, wasu hudu sun jikkata a wani hatsarin mota da ya auku a kan hanyar Gombe-Yola.
Hatsarin ya auku ne a Karamar Hukumar Kaltungo da ke Jihar Gombe a yayin da suke dawowa daga bikin auren abokin aikinsu
An garzaya da wadanda suka jikkata zuwa asibiti domin kulawar gaggawa, bayan tayar motarsu ta fashe a yankin Ladongor, tsakanin Billiri da Kumo a kan hanyar Gombe-Yola.
Hukumar Kiyaye Lafiyar Hanya (FRSC) ta Gombe ta bayyana cewa mutane 11 ne ke cikin motar Hummer da ta yi hatsarin.
Shugaban tawagar FRSC, AM Saddam, ya ce mutane biyar sun mutu, yayin da maza uku da mace ɗaya ke samun kulawa a Asibitin Kwararru na Gombe.
Ya ƙara da cewa, “An fara kai waɗanda abin ya shafa zuwa Amana Clinic da Babban Asibitin Billiri, daga bisani aka kwashe su gaba ɗaya – waɗanda suka mutu da kuma masu jikkata – zuwa Asibitin Kwararru na Gombe.”
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link