Turken Samar Da Wutar Lantarkin Nijeriya Ya Faɗi, Duhu Ya Mamaye Ko’ina


Turken dake samar da wutar lantarki na ƙasa ya faɗi a ranar Litinin sakamakon durƙushewar samar da wuta daga manyan tashoshin lantarki, lamarin da ya jefa sassa da dama na Nijeriya cikin duhu. Rahotanni sun nuna cewa turken ya faɗi ne da misalin ƙarfe 3:00 na rana.

Bayanan da aka samu sun nuna cewa samar da wutar lantarki, wanda ya kai kusan megawatt 4,800 tun da farko, ya rushe warwas zuwa megawatt 139 da misalin ƙarfe 3:00 na rana. Har yanzu ba a gano musabbabin rushewar ba.

  • Ya Zuwa Satumban Bana Adadin Lantarki Da Sin Ta Samar Ya Karu Da Kaso 17.5%
  • Ma’aikatan Wutar Lantarki Sun Yi Barazanar Tafiya Yajin Aiki A Fadin Kasar Nan

Sai dai lamarin ya faru ne yayin da Hukumar Kula da Tsarin Wutar Lantarki ta Ƙasa ke ƙoƙarin ƙara samar da wuta bayan matsalolin iskar gas da suka biyo bayan lalata bututun mai. Zuwa lokacin kammala wannan rahoto, an ruwaito cewa dukkan tashoshin wuta 22 da ke haɗe da turken ƙasa baki ɗaya sun daina aiki.

Babu wai rahoto kan dawowarsu kawo yanzu.



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *