Amurka Ta Kwace Kadarorin ‘Yan Nijeriya 8 Masu Alaka Da Boko Haram


Amurka ta kakaba wa wasu ‘yan Nijeriya 8 takunkumi, kan zargin alaka da kungiyoyin ta’addanci da suka hada da Boko Haram da kungiyar ISIL da kuma laifukan da suka shafi yanar gizo.

Ma’aikatar Baitulmali ta Amurka, ta sanar da sanya takunkumin a cikin wata takarda da ta buga ta ranar 10 ga Fabrairu, ta ofishinta na Kula da kadarorin waje (OFAC).

  • Makomar Nijeriya Na Hannun FIFA – Shehu Dikko
  • Ramadan: Lokutan Buda-Baki Da Sahur Na Azumi Na 3

Matakin yana kunshe ne a cikin shafuka 3,000 da aka sabunta na “Jerin ‘yan kasa na musamman da aka datse” (Jerin SDN), takardar bayani da ke ba da cikakken bayani ga mutane da kungiyoyin da ke karkashin takunkumin Amurka.

A cewar OFAC, suna bai wa mutanen da aka rikewa dukiyoyinsu da abubuwan da suka mallaka a karkashin dokar ta Amurka wa’adi a matsayin wani Bangare na yaki da ta’addanci da sauran takunkumi.

“Wannan littafin na ofishin baitul mali na kula da kaddarorin kasashen waje, an tsara shi ne a matsayin kayan aiki da ke bayar da ainihin sanarwar ayyukan da OFAC ke yi dangane da ‘yan kasa da aka keBe, musamman wadanda aka rike dukiyoyinsu, don taimaka wa jama’a wajen bin aiwatar da takunkumi daban-daban da OFAC ke gudanarwa,” in ji hukumar.

Daga cikin wadanda aka bayyana sunayensu, akwai Salih Yusuf Adamu, wanda aka fi sani da Salihu Yusuf, an haife shi a ranar 23 ga watan Agustan 1990. An gano yana da alaka da Boko Haram. Yusuf na daga cikin ‘yan Nijeriya shida da aka yankewa hukunci a shekarar 2022 a Hadaddiyar Daular Larabawa, sakamakon kafa kungiyar Boko Haram, domin tara kudade ga masu tayar da kayar baya a Nijeriya.

An samu kungiyar da laifin yunkurin mika dala 782,000 daga Dubai zuwa Nijeriya.

Babestan Oluwole Ademulero, an haife shi a ranar 4 ga Maris, 1953, an saka shi cikin jerin takunkumin da ya shafi ta’addanci. An gano shi a karkashin wasu da suka hada da Wole A. Babestan da Olatunde Irewole Shofeso.

An kuma nada Abu Abdullah ibn Umar Al-Barnawi, wanda aka fi sani da Ba Idrisa, wanda aka ruwaito an haife shi tsakanin 1989 zuwa 1994 a Maiduguri, Jihar Borno. An sanya shi a karkashin takunkumin da ya shafi ta’addanci.

Abu Musab Al-Barnawi, wanda kuma ake kira da Habib Yusuf, an bayyana shi a matsayin shugaban Boko Haram, kuma an bayyana shekarun haihuwarsadaga tsakanin 1990 zuwa 1995.

Khaled (ko Khalid) Al-Barnawi, an haife shi a shekarar 1976 a Maiduguri, ya fito sau biyu a cikin littafin, kuma an sanya shi cikin jerin wasu da suka hada da Abu Hafsat da Mohammed Usman.

Ibrahim Ali Alhassan, wanda aka haifa a 31 ga watan Janairun 1981, an gano cewa; yana rike da fasfo na Nijeriya, kuma an ce yana zaune ne a Abu Dhabi, Hadaddiyar Daular Larabawa. An kuma alakanta shi da Boko Haram.

Abu Bakr bn Muhammad bn Ali Al-Mainuki, wanda aka fi sani da Abu-Bilal Al-Minuki, wanda aka haifa a 1982 a Mainok, Jihar Borno, an bayyana sunansa ne bisa zargin alaka da kungiyar ISIL.

Nnamdi Orson Benson, an haife shi ranar 21 ga Maris, 1987, an sanya shi cikin jerin wadanda aka sanya wa wannan takunkumi, sakamakon wadanda ake zargi da hannu cikin masu muggan ayyuka da ke amfani da intanet. An kuma gano cewa; yana rike da fasfo na Nijeriya.

Karkashin takunkumin, an rike dukkannin kadarorin mutanen da aka lissafa a cikin ikon Amurka. Sannan kuma, an haramta wa mutanen Amurka baki-daya yin mu’amala da su.

An fitar da takunkumin ne, bisa ga umarnin zartarwa mai lamba 13224, wanda ke auna daidaikun mutane da hukumomin da ke da ruwa da tsaki a ayyukan ta’addanci da kuma bayar da kudaden ta’addanci.

A shekarar 2013 ne, Amurka ta sanya kungiyar Boko Haram a matsayin kungiyar ta’addanci ta kasashen waje.



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *