Masu iƙirarin jihadi sun kashe fararen hula 31 a Nijar

[ad_1]



Aƙalla fararen hula 31 ne suka baƙunci lahira a sakamakon wani harin ’yan bindiga da aka kai wani ƙauye da ke kusa da iyakokin Burkina Faso da Mali a yammacin Nijar.

Majiyoyin cikin gida sun ce harin ya faru ne a ranar Lahadi a ƙauyen Bosiye da ke Tillaberi — yankin da ake kira tri-border inda ƙasashen Nijar, Burkina Faso da Mali suka yi iyaka da juna.

Wani mazaunin ƙauyen ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP cewa mutane 30 sun mutu nan take, yayin da ɗaya daga cikin mutum biyar da suka jikkata ya mutu daga baya a wata cibiyar lafiya.

Kungiyar ɗalibai ta yankin ta tabbatar da harin a wata sanarwa, tana mai bayyana shi a matsayin “mugun aiki na rashin imani da tausayi”.

Kungiyoyin masu iƙirarin jihadi da ke da alaƙa da Al-Qaeda da Da’ish sun daɗe suna kai hare-hare a yankin, wanda ya shafe kusan shekara goma yana fama da rikice-rikice.

Rahoton ƙungiyar ACLED, wadda ke sa ido kan rikice-rikice, ya nuna cewa Tillaberi ya zama yankin da aka fi samun mace-mace a tsakiyar Sahel a shekarar 2025.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *