Isra’ila ta kai hare-hare a Gaza duk da kiran Trump na tsagaita wuta
[ad_1]
Hukumar kashe gobara ta yankin Gaza ta ce a ranar Asabar, sojojin Isra’ila sun kai hare-hare da dama a birnin Gaza duk da kiran da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi na a dakatar da luguden wuta bayan ƙungiyar Hamas ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta.
A ranar Asabar din nan da karfe 6 na yamma wa’adin da Trump ya bayar na cimma yarjejeniyar zaman lafiyar take cika.
“Dare ne mai tsanani ƙwarai, inda sojojin Isra’ila suka kai hare-haren sama da harbin manyan bindigogi da dama a birnin Gaza da wasu yankuna na zirin, duk da kiran Shugaba Trump na a dakatar da luguden bama-bamai,” in ji kakakin hukumar kashe gobara ta Gaza, Mahmud Bassal, yayin tattaunawa da kamfanin Dillancin Labarai na AFP.
Bassal, wanda ke jagorantar ƙungiyar agaji da ke ƙarƙashin ikon Hamas, ya ce gidaje 20 ne suka rushe sakamakon hare-haren da aka kai cikin dare.
“Yanayin ya yi tsanani ƙwarai a birnin Gaza,” in ji shi, yana mai ƙarawa da cewa ƙungiyarsu ba ta iya isa ga dukkan mutanen da abin ya shafa ba saboda “tankoki da kuma ci gaba da luguden wuta.”
Da AFP ta tuntuɓi rundunar sojin Isra’ila, ta ce tana “bincike” rahotannin hare-haren da aka kai cikin dare a Gaza.
Shirin zaman lafiya da Shugaba Trump ya gabatar a wannan makon, tare da goyon bayan Fira Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, ya ƙunshi tsagaita wuta, sakin fursunonin da ake rike da su cikin sa’o’i 72, ajiye makaman Hamas da kuma janye sojojin Isra’ila a hankali daga Gaza.
Hamas ta bayyana a ranar Juma’a cewa tana shirye ta saki fursunonin da ke hannunta bisa shirin Trump, amma ta nemi a tattauna cikakkun bayanai tare da samun damar ba da gudummawa a tattaunawar kan makomar yankin Falasɗinu.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link